hausa24-blog
hausa24-blog
Labaran Duniya hausa24h.com Daga zarar Abu yafaru
31 posts
Don't wanna be here? Send us removal request.
hausa24-blog · 6 years ago
Text
Ko Kun San Jagororin Sahawa Da Kasar Saudiyya Ta Ke Son Dakilewa?
New Post has been published on https://is.gd/Ssy4Ly
Ko Kun San Jagororin Sahawa Da Kasar Saudiyya Ta Ke Son Dakilewa?
Hukumomin kasar Saudiyya sun daura damarar dakile Jagororin Sahawa, ko kuma motsin farfadowa, a halin yanzu jagororin kungiyar uku suna garkame a hannun hukumomin, inda dukkanin su suke fuskantar hukuncin kisa, tun kafin azumin watan Ramadan babbar kotun kasar ta yankewa mutanen uku hukuncin kisa, amma ba a tsayar da hukuncin ba har yanzu, sai dai ana ganin za a iya tsayarwa a ko wani lokaci.
Da yawan masu ra’ayin na Sahawa masu sassaukan ra’ayi ne, sannan mafi yawansu suna kira ga hukumomin Saudiyyan da su sassauta tsattsauran ra’ayi da aka sansu a kai, kuma suna kira da a dinga aiwatar da hukunce-hukuncen addini Musulunci na gaskiya, ba tare da sanya ra’ayi ba.
Tun farkon kafa a kungiyar a shekarun da suka gabata, hukumomin kasar suke hararar jagororin kungiyar, yanzu abin tambaya shine; su waye jagororin Sahawa din?
Salman Al-Awdah; sanannen malamin Sunnah na kasar Saudiyya, amma mai sassaukan ra’ayi, malamin dan kimanin shekaru 60 da ‘yan kai a duniya, ya shahara da fatawoyi masu sauki, sannan ya na da mabiya a ciki da wajen kasar ta Saudiyya, hukumomin Saudiyyan sun taba garkame shi a tsakanin shekarun 1994 zuwa 1999, inda aka tuhume shi da laifin neman a kawo sauyi na siyasa a masarautar Saudiyya.
Awad Al-Qarni; Sanannen mai wa’azi, kuma malami a jami’oin Imam Muhammad Saud, da ta Sarki Khalid, masanin Shari’ar Musulunci, mai kimanin shekaru 62 a duniya. Yana daga cikin malaman da suka kalubalanci yakar kasar Iraki, kuma mai yawan goyon bayan Falasdinawa, an garkame shi tun a shekarar 2017, inda aka yanke mishi hukuncin kisa.
Ali al-Omari; mai shekaru 46 kuma dan jakadan kasar Saudiyya, sanannen ma’aikacikin gidan talabijan, kuma marubuci, tun a watan Satumban shekarar 2017 aka kama shi, inda aka zartas mishi da hukuncin kisa, bisa zargin kafa kungiyar matasa ba bisa ka’ida ba.
Safar Al-Hawali Al-Ghamdi; Dattijon malami, dan kimanin shekaru 70 a duniya, an taba kama shi a shekarar 1994 inda ya yi shekaru biyar a garkame, an sake kama shi a shekarar 2018, inda ake zargin shi da kalubalantar manufofin masarautar Saudiyya a kasashen waje, malamin ya na daga cikin malaman da suka yi fatawar wajibcin jihadi akan sojojin kasar Amurka sa suka kai hari a kasar Iraki, sannan ya kalubalanci zaman sojojin Amurkan a gabas ta tsakiya.
Nasser Al-Omar; shahararren mai wa’azi mai shekaru 67 a duniya, Farfesa a jami’ar Imam Muhammad Saud ta kasar Saudiyyan, ya na daga cikin malaman da suka rattaba hannu a fatawar tofin Allah-tsine da yakin sojojin Amurka a kasar Iraki. Malamin ya na adawa sa alakar Saudiyyan da kasar Amurka, A watan Augustan shekarar 2017 hukumomin kasar suka cafke malamin.
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
Anga jaririn watan Shawwal a kasar saudiyya
New Post has been published on https://is.gd/TGIUQZ
Anga jaririn watan Shawwal a kasar saudiyya
Hukumar kolin musulunci na kasar saudiya ta sanar da ganin jaririn Satan Shawwal da sukai a jiya,
Hakanan sadiyya ta umarci jama’ar kasarta da tsaida azumi a daren litinin yau, inda gobe zasuyi bikin sallah
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
Kanywood: Rikici ya barke tsakanin Fati Muhd da Teema biyu akan soyayyar Sen Dino Melaye
New Post has been published on https://is.gd/bDUU65
Kanywood: Rikici ya barke tsakanin Fati Muhd da Teema biyu akan soyayyar Sen Dino Melaye
Rikici ya barke tsakanin Fati Muhammed da Teema Makamashi akan soyayyar Sanata Dino Melaye
An dai ga Teema Makamashi tana habaici a shafinta na Instagram inda
Duka ‘yan matan sun yiwa Sanatan waka da fasta ta siyasa sun kai masa, inda ya dauki hoto da kowaccen su
Wani rikici da ya barke tsakanin matan Kannywood guda biyu Teema Makamashi da Fati Mohammed, inda suke rikici akan Sanatan jihar Kogi ta Yamma Sanata Dino Melaye.
Rikicin ya samo asali ne lokacin da Teema Makamashi take gargadin Fati Mohammed akan kwaikwayenta da tayi wurin yiwa Sanatan waka. Wata sabuwa: Rikici ya barke tsakanin matan Kannywood biyu akan soyayyar Sanata Dino Melaye
Wata sabuwa: Rikici ya barke tsakanin matan Kannywood biyu akan soyayyar Sanata Dino Melaye Source: Facebook
Ga abinda Teema Makamashi ta rubuta a shafinta na Instagram:
“Keda samun soyayyarsa sai dai ki gani daga nesa”
Tauraruwar Teema Makamashi wacce ita ce ta fara yiwa Sanata Dino Melaye waka, tayi wannan habaicin ne ga Fati Mohammed wacce ta kwafeta.
Teema tayi rubutun ne a shafinta na Instagram inda ta cigaba da cewa, “Ga wani sabon salon shima idan zaki yi, banda waka, tunda kome nayi sai kinyi, kina tare da bakar wahala indai ni zaki dinga kwaikwaya.”
KU KARANTA: Wata kwamiti a jihar Bauchi ta kaiwa gwamnan jihar wani tsari data binciko da zai taimaka wurin samar da ayyukan a jihar
Tauraruwar ta saka hoton fastar siyasa da tayi wa Sanatan a shafinta na Instagram a lokacin da tayi wadancan habaicin.
An ga Fati Mohammed ta yiwa Sanata Dino Melaye waka da kumaa fasta ta siyasa.
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
Hoto: Kalli Malamin dake yin luwadi da almajiransa, kuma yana bada hayarsu a Sakkwato
New Post has been published on https://is.gd/TYx7T8
Hoto: Kalli Malamin dake yin luwadi da almajiransa, kuma yana bada hayarsu a Sakkwato
Ke duniya ina zaki damu ne, yayin da ake zaton wuta a mekara sai gata an tsinceta a masaka, anan dubun wani Malamin makarantar allo ne ta cika bayan kamashi da laifin yi ma kananan yara almajirai fyade irin na luwadi, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.
Majiyar Legit ta ruwaito dalibai da dama na makarantar allon dake unguwar Arkilla a cikin garin Sakkwato sun tabbatar da cewa malaminsu mai suna Murtala Muade ya sha yi musu fyade, haka zalika sun ce yana bayar da hayarsu ga yan luwadi suna amfani dasu.
Ke duniya! Kalli Malamin dake yin luwadi da almajiransa, kuma yana bada hayarsu a Sakkwato
Maude Source: Facebook
Malam Maude ya amince da wannan zargi, sai dai yace shi yasan yara uku kacal ya taba yi ma fyade, amma an samu wasu almajirai uku da suka bayyana kansu, inda suka ce suma yana musu fyade, wanda hakan ya kawo adadin daliban da malamin yake zakke mawa zuwa shida.
Kwamishinan Yansandan jahar Sakkwato, Ibrahim Kaoje ya bayyana cewa a ranar 22 ga watan Maris ne wani lauya dake aiki da hukumar kare hakkin biladama ta kasa, Hamza Liman ya kai karar malamin zuwa ofishin DPO na Yansandan Arkilla, daga nan aka mika maganar zuwa shelkwatar Yansanda.
Kwamishinan yace duka duka shekarun yaran bai haura 4 zuwa 15 ba, kuma yawancinsu yan Zamfara ne, amma Malamin ya mayar dasu abin huce sha’awarsa, har ma yana bayar dasu haya tamkar karuwai, don haka kwamishina Kaoje ya gargadi iyaye dasu daina kai yaransu almajiranci nesa da gida.
Amma abinka da ja’irin Malami, yayin da yake ganawa da manema labaru, sai ya kada baki yace kaddara ce, dama can Allah Ya kaddara sai yayi ma almajiran nasa fyade.
Zuwa yanzu dai an garkame wannan makarantar allo, kuma Yansanda sun kaddamar da bincike akan wannan lamari mai muni, sa’annan an mika almajirai shidan zuwa ga gidauniyar ceton yara, yayin da kungiyar lauyoyi Musulmai suka dauki nauyin ciyar dasu.
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
Kwana daya da rantsar da gwamnan yobe har ya karo aure
New Post has been published on https://is.gd/PDIlA6
Kwana daya da rantsar da gwamnan yobe har ya karo aure
Sabon gwamnan jihar Yobe da aka rantsar jiya,Mai Mala Buni ya angwance kwana daya da rantsar dashi a matsayin gwamnan jihar ta Yobe inda ya auri diyar gwamnan da ya sauka ya bashi kujera.
Rahoton Daily Nigerian na cewa, Maimala Buni ya auri diyar tsohon gwamna Ibrahim Gaidam me suna Ummi Adama Gaidam a yau Alhamis inda aka daura auren cikin sirri a gidan tsohon gwamnan dake unguwar sabon Fegi, Damaturu.
Ummi da yanzu haka ke karatu a kasar Saudiyya ta zama matar gwamna Maimala Buni ta 3 kenan.
Gwamna Gaidam dai ya nuna goyon bayanshi ga Mailama Buni a takarar gwamnan jihar da yayi. Kuma rahotannin sunce Maimala Buni ne ya nemi auren Ummi ba ma tare da mahaifinta ya sani ba.
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
Ramadan: Marasa Galihu 271 Su Ka Ci Moriyar Asusun Zakka - Sheikh Argungu
New Post has been published on https://is.gd/r4B4xp
Ramadan: Marasa Galihu 271 Su Ka Ci Moriyar Asusun Zakka - Sheikh Argungu
Kimanin marayu da fakirai dari biyu da saba’in da daya (271) ne suka ci moriyar asusun zakka da wakafi na karamar hukumar mulki ta argungu a shekarar bana a karkashin jagorancin Alhaji Umar Gero Kangiwa (Sa’in Kabi).
Malam Muhammadu Ba’are (MUHAMMADU GURU) yana daga cikin bayin Allah da suka ci moriyar wannan shirin Kuma ya shedawa wakilinmu da cewa ya gode wa wannan kwamitin bisa ga irirn jajircwar da ya yi wajen ganin ya karbo zakka daga hannun attajirai ya baiwa mabukata, inda ya yi addu’ar Allah ya kara basu kwarin gwiwa wajen aiwatar da wannan aikin Kuma ya saka musu da alheri.
Shugaban kwamitin Zakka da wakafi na jihar Kabi, Dattijo Alhaji Muhammad Kwaido ya halarci taron wanda aka gudanar a fadar Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera CON. Kuma ya bayyanawa wakilinmu da cewa a wannan shekara sun soma ne da Karamar Hukumar Mulki ta Augie inda suka raba zakkar gero (hatsi) sai gundumar Gulma inda suka raba gero da kudi daga nan sai Dakingari the nda suka raba kudi sai Kuma nan Argungu inda suka raba atamfa, shinkafa man gyada da kudi ga marayu da fakirai.
Kwaido ya cigaba da cewa suna zagayen ne don su tabbatarda an baiwa wadanda Allah ya ba da umarnin a baiwa sannan Kuma ba a yi sonrai a cikin aikin ba.
Ya bayyana gamsuwarsa bisa ga yadda rabon kayan ke gudana sai dai ya nuna tashin hankalinsa bisa ga yadda mutane ke kyamar bayar da zakka duk da ya ke mabukata sai karuwa suke yi saboda haka ya yi kira ga masu hannu da shuni da su ji tsoron Allah su rinka bayar da zakka, duk da ya ke an sani suna da ‘yan uwa da mokota mabukata amma duk da haka yana da kyau su rinka tsakuro wani abu suna sakawa a asusun zakka da wakafi don kaucewa zargi.
Har wa yau dai Kwaido ya ambaci Alhaji Muhammadu Jiga Sarkin Noma a matsayin wanda ya fi kowa fitarda zakka a jihar Kebbi bisa ga kididdigar kwamitin Zakka da wakafi na jihar Kebbi saboda a duk lokacin da zai fitar da zakka sai ya nemi malamai tare da wannan kwamitin don su bayyana masa adadin da ya kamata ya fitar sannan kuma idan ya fitar yakan bayar da ita inda ya kamata.
Daga karshe Kwaido ya yi kira ga sauran kananan hukumomi da su yi koyi da Augie, Argungu, Suru, Dandi da wadansu sassa na kananan hukumomin Gwandu da Birnin Kebbi wajen farfado da kwamitocin zakka don karbo zakka da Kuma raba ta ga wadanda Allah ya ce a baiwa.
Da ya ke zantawa da wakilinmu, Sa’in Kabi Alhaji Umar Gero Kangiwa bayan kammala taron rabon kayan, ya ji dadin yadda masu hannu da shuni ke karba kira wajen sauke nauyin da Allah ya dora musu na taimakon marayu da fakirai sabanin shekarun baya inda a duk lokacin da suka je karbar zakka sai masu kudin suna bata rai wadansu Kuma kafin su bayar sai an kai ruwa rana yayanda wadansu ba su ma bayarwa.
Ya ce wannan kwamitin na mutum bakwai tun kafin azumin kowace shekara ya kan soma aiki ba dare ba rana don zakulo marayu, fakirai, miskinai da duk wadanda Allah ya bayar da umarnin a baiwa don sauke nauyin da shari’a ta dora musu.
Liman Isah Abubakar limamin masallacin izala na sabongarin Kanta ya bayyanawa wa wakilinmu da cewa wannan aikin taimakawa marayu, gajiyayyu, miskinai da zawarawa ana yin sa tun lokacin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam wanda tun wannan lokacin akan rubuta sunayen marayu ana yi musu ihsani daga aljihun baitulmali Kuma idan lokaci zakka ya yi akan ba su, hasali ma ranar da magidanci ya rasu Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam ya kan yi umarni da a kaitallafi a gidan musamman na abinci saboda a saukaka wa iyalinsa damuwa saboda haka yin haka koyi ne da shi saboda yana rage damuwa ga marayu musamman a lokacin bukin Sallah, an bayarda sutura, shinkafa da mai da kuma kudi wannan ba karamin alheri ba ne.
Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce “Mafi alhairin gida shi ne gidan da akwai maraye kuma ana tausaya ma sa haka Kuma mafi sharrin gida shi ne gidan da akwai maraye kuma a na munana ma sa.”
Saboda haka Malam Isah Abubakar ya yi kira ga shugabanni da su cigaba da wannan aikin na alheri kada su yi kasa a gwiwa saboda alheri yana sauka a cikin al’ummar da ake tausayawa marayu kuma Allah yana tsareta daga bala’o’i.
Wadanda dai su ka sami tallafin sun hada da marayu 140, fakirai 131, Guragu 40, Makafi 40, Kutare 15, sannan kuma da limamai da ladanai.
Hakazalika shi ma kwamitin tallafawa marayu na Kungiyar izala ta karamar hukumar mulki ta argungu a karkashin jagorancin Alhaji Suleman Muhammed (Jarman Kabi) da Alhaji Garba Tungar Marina (GGT) ya tallafawa marayu da dama kamar yadda yadda yadda saba a kowace shekara.
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
Magudin jarabawa: ICPC ta fara bincike kan jarabawar JAMB ta 2019
New Post has been published on https://is.gd/cLC6Pp
Magudin jarabawa: ICPC ta fara bincike kan jarabawar JAMB ta 2019
Magudin jarabawa: ICPC ta fara bincike kan jarabawar JAMB ta 2019 26 minutes ago 54 views by  Mahmoud Aliyu -Hukumar ICPC ta fara bincike domin bankado hakikanin gaskiyar lamarin da ya shafi magudin jarabawar JAMB ta 2019. -A cewar hukumar ta ICPC duk wanda aka samu da hannu cikin laifin zai fuskanci hukuncin shari’a.
Hukumar yaki da rashawa da kuma ayyuka masu alaka da ita ICPC ta fara gudanar da bincike na musamman akan magudin jarabawar da aka samu yayin rubuta jarabawar JAMB din data gabata.
Daya daga cikin mambobin hukumar ce mai suna Mrs Olubukola Balogun ta sanar da hakan ga manema labarai a wata hira da tayi da su ranar Talata a Abuja.
Magudin jarabawa: ICPC ta fara bincike kan jarabawar JAMB ta 2019 Source: Depositphotos
Tace, hukamar na kan binciken magudin jarabawar wanda akwai sa hannun iyayen yara da kuma kungiyar wasu kwararrun masu rubuta jarabawar. A cewarta hukumarsu na iya bakin kokarinta domin gano hakikanin gaskiyar lamarin.
“ Muna da niyyar yin bincike tare da yin hukunci dangane da abinda bincikenmu ya bamu. “ Muna kan yin aikin a yanzu haka domin samar wa hukumar JAMB da cikakken bayani akan magudin, ina da yakinin cewa zamuyi nasara a karshe.
“ Hukumar na kokarin sanin mene ne ya faru sannan kuma ta wace hanya za’a iya magance aukuwar hakan nan gaba,” a cewar ta. Balogun tace duk wanda aka samu da laifi zasu gurfanar dashi a gaban shari’a.
Ta bayyana magudin jarabawa a matsayin aiki na cin hanci, hukumar su tace sam baza ta bari irin wadannan miyagun ayyuka su cigaba da yaduwa a kasar nan ba. Wata majiyar da ta fito daga kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa, shugaban hukumar JAMB farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa wasu iyayen na biyawa mutane 10 su rubutawa yaronsu daya jarabawar JAMB.
“ Zaka samu cewa irin wadannan yaran bayan sun je jami’a sai kaga hotonsa ya bambamta da hoton ainihin wanda ya rubuta jarabawar.” Inji farfesa.
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
New Post has been published on http://www.hausa24h.com/rahotanni/1322186d-03c4-4975-afb2-85657814b555/27/05/2019/
“mh_magazine_options[tracking_code]”: “value”: “\n (function() \n var cx = 'partner-pub-9543466089037084:4450339849';\n var gcse = document.createElement('script');\n gcse.type = 'text/javascript';\n gcse.async = true;\n gcse.src = 'https://cse.google.com/cse.js?cx=' + cx;\n var s = document.getElementsByTagName('script')[0];\n s.parentNode.insertBefore(gcse, s);\n )();\n\n“, “type”: “option”, “user_id”: 1, “date_modified_gmt”: “2019-05-27 04:34:27”
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
New Post has been published on http://www.hausa24h.com/rahotanni/b95502b6-e999-42bf-ab13-db7ffa70fbec/27/05/2019/
“mh_magazine_options[header_transparent]”: “value”: “disable”, “type”: “option”, “user_id”: 1, “date_modified_gmt”: “2019-05-27 04:32:28”
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
Aisha buhari ta soki gwamnatin buhari
New Post has been published on https://is.gd/sHK8tW
Aisha buhari ta soki gwamnatin buhari
Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta ce shirin bayar da tallafi na gwamnati (SIP) da Uwargida Maryam Uwais, mai taimaka wa shugaban kasa a kan shirin tallafi, ke jagoranta, ya gaza a yankin arewa.
Da take magana ranar Asabar yayin wani taro da aka yi a fadar shugaban kasa, Aisha Buhari ta ce an fada mata cewar kimanin mata 30,000 ne daga jihar Adamawa zasu ci moriyar shirin amma sai gashi hakan ta gaza yiwuwa.
Da take magana a kan Uwargida Maryam, Aisha Buhari ta bayyana cewar an ba ta mukamin ne tun farko domin saka wa Kanawa a kan miliyoyin kuri’un da suka zazzaga wa mijinta a zaben shekarar 2015 ‘Yar asalin jihar Kano, Uwargida Maryam, mata ce ga tsohon alkalin alkalan Najeriya, Jastis Mohammed Lawal Uwais.
“Biliyan N500 da gwamnati ta ware wa shirin SIP na daga cikin alkawuran da jam’iyyar APC tayi na ciyar da dalibai a makarantun firamare da bawa mutanen da talauci ya dama tallafin N5000 duk wata.
“Mai taimaka wa miji na a kan shirin macece ‘ya asalin Kano, wacce na tabbata ya bata mukamin ne domin saka wa mutanen Kano a kan kuri’un da suka bashi a zaben shekarar 2015. Ban taba tambayar yadda ake amfani da kudin da gwamnati ta ware ba.
“Na taba haduwa da daya daga cikin hadiman jagoran shirin SIP wanda ya yi min alkawarin cewar za a ke bawa mata 30,000 N10,000 kowanne wata, amma har yau ba a yi hakan ba kuma ban kara ji daga gare shi ba,” a cewar uwargidan ta shugaban kasa.
“Ba zan yi magana mai tsawo ba don kar a ce ina sukar gwamnati ko na cika surutu amma ni na san alkawarin da muka daukar wa jama’a shine za ake bawa talakawa futik tallafin N5,000 kowanne wata amma sai gashi da na je Kano naga wani dattijo da ke sayar da kayayyaki da yace jarinsa bai fi 3,000 zuwa 4,000 ba.
“Ban san a wanne wuri shirin ya yi tasiri ba amma dai a arewa, musamman a jihar Adamawa, shirin bayar da tallafin bai amfani jama’a ba. Karamar hukuma daya ce a cikin 22 ta ci moriyar shirin.
Hatta a jihar Kano shirin bai tabuka komai saboda mata dake kananan sana’o’i basu samu tallafin komai ba,” a cewar Aisha Buhari.Rariya
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
Masu garkuwa da mutane sun kashe shugaban fityanul islam dake karamar hukumar jama'a a jihar kaduna
New Post has been published on https://is.gd/ehJ10K
Masu garkuwa da mutane sun kashe shugaban fityanul islam dake karamar hukumar jama'a a jihar kaduna
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN Yanzu muka samu labarin cewa an tsinci gawar Shugaban Kungiyar Fityanul Islam na karamar hukumar Jama’a dake jihar Kaduna. 
Dama tun makonni biyar da suka gabata wasu mutane wadanda ake tasamanin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da shi, mun samu labarin an tsinci gawar shi a safiyar yau. 
Muna mika ta’aziyya a madadin kungiyan fityanul Islam gaba daya.
Allah ya jikansa ha gafara masa yasa aljanna ce makomarsa, su kuma wadannan miyagun Allah ya tona asirinsu, amin
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
KANNYWOOD: Masu Garkuwa Sun Sako Mataimakin Shugaban MOPPAN
New Post has been published on https://is.gd/xP5nm4
KANNYWOOD: Masu Garkuwa Sun Sako Mataimakin Shugaban MOPPAN
yanzu-yanzu sun tabbatar da cewa, masu garkuwa da mutane sun sako Mataimakin Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa, MOPPAN, na kasa, wato Malam Salisu Mu’azu tare da sauran mutane biyun da su ke tsare da su.
Mun ba ku rahoton cewa, a ranar Alhamis ne dai a ka kama su kan hanyarsu ta zuwa Jos bayan kammala wani taro a Kaduna, inda lamarin ya afku bayan an wuce Jangere daidai kauyen Saya. An kama shi ne tare da abokan aikinsa, Malam Danlami Yanke-yanke da Malam Andy Bature, inda kuma yayansa, Alhaji Sani Mu’azu, ya sha da kyar.
Rahoton ya nuna cewa, a yanzu su na kan hanyarsu ta zuwa asibiti a cikin garin Jos, domin duba lafiyar Malam Salisun, wanda a ka ce ya na cikin wani yanayi na halin rashin lafiya.
KARIN BAYANI:
Yanzu haka an gama duba lafiyar Malam Salisu Mu’azu har ya koma gida cikin iyalinsa.
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
Cikakken sunayen yan takarar PDP a Zamfara da suka lashe zabe bayan faduwar APC
New Post has been published on https://is.gd/PCnwB2
Cikakken sunayen yan takarar PDP a Zamfara da suka lashe zabe bayan faduwar APC
Kafin ranar Juma’a, 24 ga watan Mayu ana yiwa dukkabin yan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019 a jihar Zamfara kallon wadanda suka sha kaye a zabe, sai dai hakan ya sauya a yanzu bayan hukuncin kotun koli da ta soke kuri’un yan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gaba daya.
Kotun koli ta kaddamar da cewa APC a Zamfara bata da yan takara a zaben 2019, don haka ba za ta iya ikirarin lashe zaben ba.
Majalisar alkalai biyar, karkashin jagorancin Ibrahim Muhammad, mukaddashin shigaban alkalan Najeriya, ya zartar da cewa a kaddamar da wadanda suka zo na biyu a zaben a matsayin wadanda suka lashe zaben idan har sun cike sharudan kundin tsarin mulki. Cikakken sunayen yan takarar PDP a Zamfara da suka lashe zabe bayan faduwar APC
Cikakken sunayen yan takarar PDP a Zamfara da suka lashe zabe bayan faduwar APC Source: Twitter
Hukuncin ya yi aiki me akan PDP wacce ta zo ya biyu a zaben.
Ga cikakken jerin sunayen yan takarar jam’iyyar PDP a Zamfara wadanda suka yi takara a zaben:
Gwamna
Bello Matawalle
Mataimakin Gwamna
Mahdi Gusau
Majalisar dattawa
Ya’u Sahabi, Zamfara north
Mohammed Hassan, Zamfara central
Lawani Hassan, Zamfara West
Majalisar wakilai na tarayya
Umar Dan-Galadima – Kaura-Namoda/Birnin Magaji federal constituency
Bello Hassan Shinkafi – Shinkafi/Zurmi federal constituency
Kabiru Amadu – Gusau/Tsafe federal constituency
Shehu Ahmed – Bungudu/Maru federal constituency
Kabiru Yahaya – Anka/Talata Mafara federal constituency
Ahmed Bakura – Bakura/Maradun federal constituency
Sulaiman Gum – Gummi/Bukkuyum federal constituency
Majalisar dokokin jiha
Zaharadeen M. Sada – Kaura Namoda north constituency
Kaura Namoda – south constituency
Nura Daihiru – Birnin Magaji constituency
Salihu Zurmi – Zurmi east constituency
Nasiru Muazu Zurmi west constituency
Muhammad G. Ahmad – Shinkafi constituency
Musa Bawa Musa – Tsafe east constituency
Aliyu Namaigora – Tsafe west constituency
Ibrahim Naidda – Gusau east constituency
Shafiu Dama – Gusau west constituency
Kabiru Magaji – Bungudu east constituency
Nasiru Bello Lawal – Bungudu west constituency
Yusuf Alhassan Muh – Maru north constituency
Saidu Umar – Maru south constituency
Yusuf Muhammad – Anka constituency
Shamudeen Hassan – Talata-Mafara north constituency
Aminu Yusuf Jangebe – Talata-Mafara south constituency
Tukur Jekada – Bakura constituency
Faruk Musa Dosara – Maradun I constituency
Nasiru Atiku – Maradun II constituency
Abdulnasir Ibrahim – Gummi I constituency
Mansur Mohammed – Gummi II constituency
Ibrahim Mohammed Naidda – Bukkuyum north constituency
Sani Dahiru – Bukkuyum south constituency
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
Untitled Reusable Block
New Post has been published on http://www.hausa24h.com/rahotanni/untitled-reusable-block/25/05/2019/
Untitled Reusable Block
KU KARANTA KUMA: Yadda rikicin jam’iyyar APC ya samo asali a jihar Zamfara
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
New Post has been published on http://www.hausa24h.com/rahotanni/8f031d14-4ac5-4573-8d8e-e7b35636a96e/25/05/2019/
“mh_magazine_options[content_ad]”: []).push();\n“, “type”: “option”, “user_id”: 1, “date_modified_gmt”: “2019-05-25 08:04:05”
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
New Post has been published on http://www.hausa24h.com/rahotanni/4a0ab817-83bf-4974-a8d7-61f7eab815b4/25/05/2019/
“mh_magazine_options[widget_layout]”: “value”: “layout8”, “type”: “option”, “user_id”: 1, “date_modified_gmt”: “2019-05-25 08:00:42” , “mh_magazine_options[loop_layout]”: “value”: “layout5”, “type”: “option”, “user_id”: 1, “date_modified_gmt”: “2019-05-25 08:00:42”
0 notes
hausa24-blog · 6 years ago
Text
New Post has been published on http://www.hausa24h.com/rahotanni/1867e615-9e1f-4f08-b226-757d375722e9/25/05/2019/
“mh_magazine_options[font_body]”: “value”: “playfair_display”, “type”: “option”, “user_id”: 1, “date_modified_gmt”: “2019-05-25 07:56:29”
0 notes