Don't wanna be here? Send us removal request.
Photo

GORON SAHUR; TARIHI👇 GARIN SODOM, GARIN MUTANEN ANNABI LUT(A.S); ...Kamar Yanda ALLAH(S.W.T) Yayi Alkawarin Wanzuwar Wannan Wurin Da Aka Halakar Da Mutanen Zamanin ANNABI LUT(A.S) Don Ya Zama Izina Da Wa'azi Har Tashin Qiyama Ga 'Yan Baya, Har Yanzu Haka Wurin Yana Nan Yanda Yake, Kuma Kowanne Lokaci Al'umma Daga Sassan Duniya Daban-Daban Suna Zuwa Don Ganewa Idonsu, Ikon ALLAH🙏 Wancan Da Ake Gani Kamar Dutsi a Tsaye, Masana Tarihi Sun Tabbatar Da Cewa; Matar ANNABI LUT Ce, Wanda Ita Ma Tana Cikin Wadanda Fushin ALLAH(S.W.T) Ya Tabbata Akansu, Sunan Wurin/Garin SODDOM, Yanzu Haka Yana Can a Cikin Kudancin Kwarin Kogin Jordan, Kimanin Kilomita 14(9 Ml) Arewa Maso Gabas Da Tekun Gishiri, Ma'ana Wajen Yanzu Yana Cikin 'Kasar Jordan 🇯🇴. A Gabas Ta Tsakiya. ALLAH Ya Ƙara Mana Ƙarfin Imani, Ya Kiyaye Mana Imaninmu, Don Albarkar SHUGABA(S.A.W)🙏🙏🙏 (at Nigeria) https://www.instagram.com/p/CqcLuaVoeqW/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

YADDA MALAMI MAI YIN TAFSIR YAKAMATA YA ZAMA KAFIN YA FARA YIN TAFSIR Da farko dai mutum barai fara yin tafsir ba sai idan ya san ya wadannan Abubuwan kafin ya fara yin tafsir Reshin sanin wadannan Abubuwan shi yake kawo zagi da kage a cikin tafsirin mai yinsa Abubuwan sune guda 14: 1. Ya zama Mahaddacin Al-qur'ani 2. Ya zama Mahaddacin wasu daga Hadisai atleast ko 2500 zuwa 3000 3. Ya zama yana Duba Tafsiran Malamai magabata sosai 4. Yasan Furu'a kuma ya karanta Furu'a saboda sanin Ahkamu wato hukunce hukuncen Addini 5. Yasan Luggan Larabawa wato Larabci 6. Yasan Tasauwuf, Don samun gada a Tafsirin sa 7. Yasan Nahawu/lirabi 8. Yasan Usulul Fighu 9. Yasan Usulul Dinu 10. Yasan fannin Balaga 11. Yasan Asbabun Nuzul 12. Yasan Nasikh da Mansukh 13. Yasan Tarihin Addinin Musulunci wato "Siyar 14. Yasan Ilmul Qiraa'aat Ko da shike IMAMU ASSUYUDI yace Abubuwan sun kai Almost 50 to 55 Amma wadannan 14 sune Manyan a lamarin Addini To in mutum bai san su ba bai kamata ya ajiye littafi a gabansa wai da sunan yana tafsir ba Don haka akiyaye mu expecially masu yin tafsiri a Adamawa Via: Umar Chobbe✍️ (at Nigeria) https://www.instagram.com/p/Cqaa1oVo_56/?igshid=NGJjMDIxMWI=
1 note
·
View note
Photo

...Na Ga Masu Arziki Irin Wanda Nake Burin Na Yi, Sun Yi Amma a Ƙarshe Sun Talauce. Sai Na Ce; ALLAH Ka Sa Idan Na Yi, Ka Da Na Yi Alfahari, Kuma Na Yi Kyauta Na Yi Sadaka, Tunda Na Gane Shi Arzikin Baya Tabbata, Ko Ya Tabbata, Mai Shi Baya Tabbata, Amma Shi Alherin Da Aka Yi Da Shi(Arzikin) Ka Iya Tabbata. Othman Muhammad ✍️ ALLAH Ka Ƙara Mana Wadatar Zuciya, Ka Ƙara Mana Rufin Asiri Don Arzikin SHUGABA(S.A.W)🙏🙏🙏 (at Nigeria) https://www.instagram.com/p/CqaR68OITg_/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

"...Duk Wanda Yayi Imani Da ALLAH Da MANZONSA, To Ya Karrama Baƙonsa.... RAMADAN Baƙo Ne, Sai Mu Duba Mu Ga Dame Ya Kamata Mu Karrama Shi.... Wannan Wani Wata Ne Da UBANGIJI Na Ya Girmama Shi, Don Haka NI Nafi Cancanta Da Na Girmama Shi..." Imamu Shibliy(R.A)🙏 ALLAH Ya Sada Mu Da Dukkan Alkhairan Dake Cikin Wannan Watan Na RAMADAN, Ameeen🙏🙏🙏 BARKANMU DA SHAN RUWA👌🙏🙏 (at Nigeria) https://www.instagram.com/p/CqYlTxPoHMA/?igshid=NGJjMDIxMWI=
1 note
·
View note
Photo

AL-MA'ARUF CHARITY FOUNDATION👌🙏👇 Wannan Gidauniya Ce Da Aka Samar Da Ita Cikin Ikon ALLAH, Don Gudanar Da Ayyukan Alkhairi Musamman Kamar Taimakon Marayu, Gajiyayyu Da Mabuƙata. Wannan Ya Sa Gidauniyar Ta Ƙuɗiri Aniyar Samarwa Marayu, Gajiyayyu Da Mabuƙata Kayan Sallah Duba Da Halin Da Ake Ciki Na Matsi. Al'umma Zata Yi Daraja Ne, Idan Na Sama Yana Taimakon Na Ƙasa Da Shi. Yaya Kake Gani Idan Zaka Bayar Da Abin Da ALLAH Ya Hore Maka Ba Tare Da Ka Raina Abin Da Za Ka Bayar Ba??? Wannan Gidauniya Ta Yi Haramar Ɗinkawa Marayu, Gajiyayyu Da Mabuƙata Kayan Sallah a Jihohin; Kano, Katsina, Yobe, Kaduna da Jos, Domin Faranta Musu Da Niyyar Duk Wanda Ya Saka Jarinsa a Ciki ALLAH Ya Mayar Masa Ta Inda Bai Yi Zato Ba Duniya Da Lahira. Ga Duk Mai Buƙatar Karin Bayani Zai Iya Tuntuɓar Waɗannan Lambobi Kamar Haka👇👇👇 08038001563 Malam Usman Bin-Affan 08069917239 Muhammad Usman Gashua Ga Wanda Kuma Zai Turo Gudunmawarsa, Kai Tsaye Zai Iya Turawa a Wannan Lambar Bankin👇👇👇 Lambar Asusu: 3129274121 Sunan Mai Asusu: Adamu Suleiman Sunan Banki: FirstBank. ALLAH Ya Bada Ikon Taimakawa, Don Albarkar SHUGABA(S.A.W)🙏🙏🙏 (at Nigeria) https://www.instagram.com/p/CqXmENTIKbI/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

...Haɗuwa Da MUTANE(Kowaɗanne Iri Ne) RIBA Ce; *1. Su, Na Ƙwarai Zaka Amfana Da Su. *2. Su, Kuma Miyagu Zaka Koyi Darasi Daga Rayuwarsu. ALLAH Yayi Mana Mana Jagora a Dukkanin Al'amuranmu, Don Alfarmar SAYYIDUL-WARA(S.A.W)🙏🙏❣️ BARKANMU DA SHAN RUWA🙏🙏❣️ https://www.instagram.com/p/CqWH4tHog7b/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

WANDA YA TAIMAKI WANI.....😭😭👏👏🙏🙏🙏 Wannan Baiwar ALLAH Marainiya Ce, Iyayenta Duk Basa Raye, Mijinta Kuma Ya Gujeta Ya Bar Mata Yara. An Koreta Daga Gidan Haya Saboda Ba Kuɗin Da Zata Biya, Shi Ne Take Buga Bulo Na Laka Domin Ta Gina Matsugunin Da Zata Zauna Ita Da Yaranta a Filin Da Ta Gada a Gurin Mahaifinta. Tana Zaune a Hayin Rigasa a Garin Kaduna, Wanda Yake Son Ya Je Ya Ga Halin Da Matar Take Ciki(Ko Neman Ƙarin Bayani) Sai Ya Ƙira Waɗannan Layukan Waya👇 O7084113798 07037128035 Wanda Zai Taimaka Da Kuɗi Kuma Ga 'Account Number'👇 1638117283 Access Bank Khanasar Abubakar Abdullahi Waɗannan Hotunan An Ɗauka Su Ne a Jiya Litinin, Kuma Da Azumi a Bakin Matar Take Aikin Buga Bulon Domin Ta Gina Ɗaki. 'Yan-uwa Musulmi Mu Taimaki Rayuwar Wannan Baiwar ALLAH Da Abinda Ya Sauwaƙa Albarkacin Watan Ramadan Mai Tarin Falala🙏 Muna Rokon ALLAH Ya Rufa Mana Asirin Duniya Da Lahira, Don Albarkar SHUGABA(S.A.W)🙏🙏🙏 (©️Shehu Dawood Al-Dawoody Funtua✍️✍️✍️). https://www.instagram.com/p/CqVvI1cIB5B/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

GORON SAHUR👇👇👇 "AN TADA GAWA, HAR MA YA CI ABINCIN DA AKA DAFA DON ZAMAN MAKOKINSA"; SAYYIDI BASHIR IBN MAULANA SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI(R.A) Yana Cewa; "An Samu Wata Gyatuma/Tsohuwa Da Ta Yi Hijra Daga MAKKAH Zuwa MADINAH Ta Biyo MANZON ALLAH(S.A.W), Don Ta Samu Cikawa Mai Kyau, Ita Wannan Gyatumar Akwai Ɗanta Ƙarami Ana Ƙiransa Da Suna; THABIT Da Ta Taho Da Shi(Daga Makkah), Shi Wannan Yaron Sai ALLAH Yayi Masa Rasuwa, Har An Shirya Shi Ana Shirin Akai Shi Maƙabarta, Sai Ga MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Iso Wajen Don Yi Mata Ta'aziyya(Na Rashin Wannan Yaron Nata), Da Ganin MANZON ALLAH(S.A.W) Sai Ta Zabura Ta Ce; "Ya RASULULLAHI! Ba Ta'aziyya Nake So(Daga Wajenka Ba) Ina So Ne Ka Nuna Min Mu'ujizarka Yau, Ka Taimaka, Ka Tayar Min Da Yaron Nan, Wallahi Shi Ɗaya Ne Ƙwal a Wurina, Bani Da Kowa Sai Shi Kaɗai", Sai MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Dubi Wannan Yaron Yana Cikin Likkafani Yana Jiran a Binne Shi Sai Ya Ce; "THABIT TASHI!", Nan Take Yaron Nan Ya Miƙe Ya Tsaya, ANAS BN MALIK(R.A) Ya Ce; "Abincin Da Aka Dafa Ma Don Makokinsa, Da Shi Yaron Aka Ci Abincin". Othman Muhammad ✍️ YA ALLAH! KA ƘARA MANA ZUNZURUTUN SOYAYYAR SAYYIDUL-WUJUDI(S.A.W), KA AZURTA MU DA ZAMA A ƘARKASHIN INUWARSA(S.A.W) A GOBE QIYAMA YA ALLAH AMEEEEEEN❣️🙏🙏 https://www.instagram.com/p/CqUiq9iofVN/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

Mafiya yawan matasa suna yin asarar ladan azuminsu ta hanyoyi da dama. Misali kamar: QARYA: ANNABI (S.A.W) yace: "DUK WANDA BAI BAR QARYA DA QAULUZ ZUR DA KUMA AIKI DA ITA BA, TO BABU RUWAN ALLAH DASHI DON YA BAR ABINCINSA DA ABIN SHANSA". Amma zaka ga Matasa da dama sun zauna a Majalisai da wuraren zamansu, amma basu da wani aiki sai Gulma, Qarya, zancen Mutane, da kuma yada Jita-jita. Duk mai yin haka idan bai dena ba, aranar Alkiyamah ba zai samu ladan azumi acikin Mizaninsa ba. Wannan sakon Yana zuwa muku ne daga taskar Umar Chobbe✍️ Allah shi kiyayemu, Allah shi karbi dukkan Aiyukanmu, kuma ya gafarta mana dukkan Zunubanmu Gaba Daya Albarkan ANNABI S.A.W https://www.instagram.com/p/CqTXuA2IkWr/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

#FLASHBACK👇👇👇 SHEHU TAHIRU(R.A) ....An Yi Tafsiri a Shekarar 1981, Aka Yi 1982 Aka Yi 1983, Kawai Sai Marigayi Malam Abubakar Gumi Ya Ce: "Ai Rauhanai Ne Yake Amfani Dasu, A Jikin Tasbahansa(Carbi) Suke..." Ai Kuwa Da Shekara Ta Zagayo a Shekarar 1984 Sai MAULANMU SHEHU TAHIRU(R.A), Ya Ce: "An Ce Wai Muna Riƙe Tasbaha/Carbi Da Rauhanai a Jiki, To Mun Ajiye Carbin...!". To Daga Wannan Shekarar Ne Fa; MAULANMU SHEHU TAHIRU(R.A) Ya Fara Yin Tafsirin SUNNAH, Wato Da Ka(Ba Tare Da Kallon Littafi Ba), Har Yau Ɗin Nan. Othman Muhammad ✍️ ALLAH Ya Ƙara Lafiya Da Nisan Kwana MAULANA SHEIKH(R.A), Ya Bamu AlbarkarKU🙏🙏🙏 https://www.instagram.com/p/CqS4P71oXLQ/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

REPORT👇 Around 800,000 People Prayed Shoulder To Shoulder Last Night In Tarawih Prayer At Al-Hassan II Mosque In Casablanca, Morocco🇲🇦. This Mosque Is The Largest And One Of The Most Beautiful Mosque In Africa🌍 In Prayer; Rich And Poor, Old And Young, Black And White Take Equal Space And Equal Role To Form a Wall Of Unity From The Lines Described In The Qur'an As Layed Bricks. This Is The Beauty Of Islam😍❤️ Alhamdulillah☝🏻❣️🙏 https://www.instagram.com/p/CqSvu9fIm2r/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

BARKANMU DA SHAN RUWA: MAULANMU SHEHU AHMADU TIJJANI(R.A) Yana Cewa: "Duk Wanda Ya Aikata Ɗaya Daga Cikin Waɗannan Zunuban(Idan Bai TUBA Ba) Zai Mutu Babu IMANI: *1. Wanda Yayi Ƙaryar Walittaka, *2. Bayar Da Wuridi/Ɗarika Ba Tare Da Izni Ba, *3. Yawan Cutar Da/Zaluntar Mutane, *4. Yawan Zina, *5. Yiwa MA'AIKI(S.A.W) Ƙarya/Ƙirkiran Hadisi Na Ƙarya a Jingina Shi Ga MA'AIKI(S.A.W), *6. Yawan Annamimanci Da Giba, *7. Wulaƙanta/Tozartar Da Mahaifa". ALLAH YA KARE MU BAKI ƊAYA DA ZURI'ARMU, YA AZURTA MU DA CIKAWA DA IMANI AMEEEEEEN❣️🙏🙏 https://www.instagram.com/p/CqQ_KHwI7VO/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

A RANA MAI KAMAR TA JIYA (25-03....)👇👇👇 A Rana Mai kamar Ta Jiya, Amma Ta; 25 Ga Watan Maris 1975, Wasu Mahara Suka Harbe SARKI FAISAL Na Ƙasar Saudi Arabia 🇸🇦 Har Lahira. SARKI FAISAL Dai Ya Kasance Masoyin Gaske, Kuma Hadimi Ga SHEHU IBRAHIM NIASSE(R.A). Kuma Dukkansu Sun Koma Ga MAHALICCINSU a Shekara 'Daya, Wato; 1975. Don Haka; Masoyin Masoyinmu, Masoyinmu Ne.......❣️❣️🙏 Othman Muhammad ✍️ ALLAH Ya Jaddada Rahama Ga SARKI FAISAL, Ya Gafarta Masa Kura-Kurensa, Ya Bamu Albarkar Masu Albarka, Ameeen🙏🙏🙏 https://www.instagram.com/p/CqQzMpbIkSW/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

HUKUNCIN NIYYA Niyya Wajibi ce a duk Azumin Farilla ko Azumin da yake na wajibi ne kamar na ramuwa da kaffara saboda fadin Annabi Muhammadu S.A.W. "Dukkan Ayyuka sai da niyya". Kuma mutane su fahimci hadisin da Sayyida Hafsat R.A. Matar Annabi Muhammadu S.A.W. Ta ruwaito cewa: ANNABI S.A.W. Yace: "Wanda duk bai dauki niyya kafin Alfijir ba to ba shi da Azumi". Abu Dawud Ne Ya Ruwaito Shi. Ya halatta a dau niyya a kowanne lokaci a cikin dare ko da sauran minti daya Alfijir ya fito. Niyya ita ce: "Kudurce yin Azumi a gobe". Kuma Niyya daya ta wadatar da watan Ramadan, sai dai idan wani abu ya san an dakatar da Azumin, to sai a sake yin niyya", wannan shi ne ra'ayin Malaman Malikiyya, kuma shi ne mafi inganci". Wannan sakon Yana zuwa muku ne daga taskar Umar Chobbe✍️ Allah ya Bamu Alkhairin dake Cikin Wannan Watan Mai Albarka Bijahi S.A.W (at Nigeria) https://www.instagram.com/p/CqQtXqIIPUp/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

...Shi AZUMI; Kamar Girki Ne, Idan Ya Ji Kayan Haɗi Ya Fi Ƙamshi Da Tasiri a Jiki. AZUMIN Da Ya Haɗu Da👇👇👇 Qur'ani, Yawaita Sallar Nafiloli, Ciyarwa, Zumunci, Da Salati, Da Sauransu, Ya Fi Wanda Bai Samu Waɗannan Kayan Haɗin Ba Ɗand'ano, Garɗi, Tasiri a Zuciya, Da Daraja a Wajen ALLAH(S.W.T). ALLAH Ka Sa Muna Daga Cikin Bayin Da Za'a 'Yantar a Cikin Wannan Watan Na Ramadana Ameeeeen. RAMADAN KAREEM🙏🙏♥️ https://www.instagram.com/p/CqQeSOMIgQi/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

GORON SAHUR...👌🙏👇 SAYYIDUNA ALI(K.W) Ɗaya Ne Daga Cikin Mutane Goma Da Aka Yi Masu Bushara Da Aljanna Tun a Duniya. Bai Ta6a Yiwa Gunki Sujjada Ba Tunda ALLAH Ya Halicce Shi. Shugaban Masu Gudun Duniya. Mafi Shahara a Wajen Khuduba. (©️Imam Assyudi-Tarikhul Khulafa). ALLAH Ka Yi Salati Da Tsira Ga ANNABI MUHAMMADU Da Iyalan Gidan Shi Tsarkaka Albarkacin Salatin Nan ALLAH Ka Yi Tajallin Jamala a Cikin Dukkan Al'amurranmu💔🙏🙏 https://www.instagram.com/p/CqPZ0iaoY5R/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Photo

Duk wani abu da kaga munayi "Kame-Kamene bayan farillanmu na wajibi" tabbaci da yakininmu ya tabbata cikin soyayyar BAHASHIMIN DANGI (S.A.W) ko da zamu rasa komai a rayuwa, ALLAH kada a jarabcemu da Talaucin Soyayyar MANZON ALLAH (S.A..W)...! https://www.instagram.com/p/CqObounIPV2/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes