Tumgik
#hana kira nika
lilietsblog · 6 years
Photo
Tumblr media
when I said I was going to go do that did yall think I was joking because I wasn’t
I know almost nothing about precure (which is what the character creator is apparently based on) but IT HAS NOTHING TO DO WITH MY COOL NEW MAGICAL GIRL OCS ANYWAY
left to right, these are Hana, Kira and Nika
Hana wields the element of Darkness: dampening others’ powers, literally shutting out light (she can still see / sense things herself) and occasionally influencing / dampening people’s thoughts / emotions. Calming people down, derailing trains of thought, up to and including actual memory wipes. Her power has pretty much no offensive element, but she’s a support powerhouse and can literally handle a fight by herself by slowly winding it down to the end
Kira wields the element of Fire: literally setting things on fire, raising temperature of an area or an object, manipulating existing fires; on an emotional level, distracting people and pissing them off (specifically as a power effect, essentially drawing aggro); and finally, speeding herself up and resistance to heat which  extends to her post-transformation outfit. Her power is very strongly offensive but her only defense (other than ‘offense is the best defense’) is mobility, so she still needs others’ support to be safe in a fight.
Nika wields the element of Ice: creating ice out of thin air, lowering temperature of objects and areas, resistance to cold; on a more abstract level, she can ‘freeze herself out of reality’, which has a number of effects which she can turn up and down to a degree: - lowering the impact others’ powers have on her, while her own power remains at the same strength if a bit more difficult to control; - making herself harder to both notice and remember, ‘fading’ out of reality on perception level; - reducing the impact of physical interactions with the world, up to being able to literally pass through solid objects. Her power is versatile both offense and defense wise, but has a number of drawbacks that make it her strong preference to not fight alone.
Their powers have interactions, intuitively obvious for Nika and Kira together (manipulating temperatures of anything freely in any direction, creating water) (Kira herself cannot put out fires she starts, only move them around, and Nika cannot reduce the amount of ice she’s already created) and significantly more abstract for Hana. The intertwine of her power and Kira’s enables them to heal people, and the intertwine of her power and Nika’s enables them to mend objects - and on the other end of the spectrum, she can make both Kira’s flames and Nika’s ice more deadly/injurious/destructive, basically reducing resistances living creatures and objects have to them.
Their powers ‘wind up’ as they use them, and the longer the fight, the bigger guns they’re able to pull, often surprising themselves (and occasionally putting themselves in danger). All three of them have a connection to a ‘plane’ of their element, and can fly by forging a ‘path’ through the air that brings in some of that plane into the real world, enabling them to move through it freely. Hana uses this ability most freely, in no small part due to essential harmlessness of her element: she can practice with impunity, without worrying about either killing something with frost or setting anything on fire. Kira makes up for lack of practice with enthusiasm, counting on the interaction of her power and Nika’s to cancel out her ‘heat trail’, and Nika prefers to stay on the ground or make ice ‘platforms’ to run/jump across (their inherent connection to their plane prevents her from slipping or losing her balance)
After a bit of practice with transformation, all three of them are capable of using their powers while detransformed; however, as far as the ‘winding up’ effect goes, they start at a very, very low level of strength - transformation essentially jump starts it, along with giving them stylish looks. There’s more to it, however: the mechanism by which it does that is by making them less human and closer to an ‘elemental’ of their element, which can have a number of drawbacks,which grow as their power winds up. This is particularly noticable for Nika, who is not a fan of the effect ‘fading out’ has on her despite appreciating its utility. The most immediate and noticable effect is on their emotions. Ironically, to a degree, this is most harmless for Hana, who simply becomes more tranquil and less capable of focus as a counterbalance to her perception expanding otherwise, and she actually likes this state. Kira’s expanding connection to her element makes her more reckless, prone to tunnel vision and less empathetic; she makes sure to focus on listening to her teammates’ directions as her power grows. The effect on Nika is weaker than the other two if she doesn’t ‘fade out’ and stronger if she does, leaving her more consciously aware of it: it dissolves her attachments and strong emotions, figuratively freezing her heart. For all three of them, going too far into this state can lead to losing themselves, their identities and memories, and while detransforming restores them to a baseline human state, it’s still a traumatic experience. As their control over their power grows, they’re able to access higher levels of strength with less emotional blowback, and control the speed at which their power ‘winds up’, allowing them to possibly spend days at a time at a just-post-transformation baseline or wind up to the highest safe tier within minutes.
Their transformation trinkets take shape of friendship bracelets, which change their design with time based on their growth / emotional states. Originally they were actual friendship bracelets the three made together. They were not very close friends, but their shared affinity for magic brought them together until they made a physical embodiment of this connection, which then became a physical embodiment of their connection to magic, too.
As far as interpersonal dynamics go, Nika is kind of the ‘center’ of the team in that she’s the person both Kira and Hana are unambiguously friends with. She’s sweet, nice and non-confrontational, and cares about harmony between the three of them more than anything. Kira has aspirations of a leader, coming up with plans and pushing the group to be more proactive, while Hana acts as a check on her overflowing initiative, holding her back and serving as a voice of reason, which frequently leads to tension between the two of them. Their respect for each other grows with time, but they still occasionally have difficulty overcoming their stubborn natures and communicating properly without Nika to serve as a mediator.
(without Kira, Hana and Nika tend to sit on their hands and wait for ideas/fights/initiative to come to them, and have to deliberately and determinedly collaborate to actually come up with a proactive plan)
(without Hana, Kira pulls pliant Nika along into all kinds of explosive trouble, that they coincidentally cannot easily mend side effects of without Hana’s powers, and have to go through a lot of trouble to at least mitigate)
Their transformation does not affect their facial features and body shapes (other than giving them animal attributes) but it significantly alters both their hairstyle and manner of dressing. Kira’s style is actually most similar to her post-transformation one, as she likes wearing girly but practical clothes, with cute wide skirts with modesty shorts underneath as a staple; but her hair is cut short, without bangs, which makes her look significantly enough different to be just short of unrecognizable from a distance. Hana’s hair is usually up in elaborate ‘dos, similar to Nika’s post-transformation one, and her parents tend to dress her in overly feminine (to her taste) jewel-toned clothes that look nothing like her post-transformation outfit. Nika simply has no sense of style / fashion sense / ability to dress herself, and usually wears jeans & cartoon t-shirts with her hair in a simple braid and her bangs clipped back. For all three girls, their post-transformation outfits are essentially how they’d like to dress if neither practicality nor other people’s opinions were a concern.
Their animal attributes do have significance beyond making them even cuter, and symbolize their connection to specific presiding deities. This connection is independent of their element and is in fact specifically the thing that allows them to control it, transform back and forth and not succumb instantly to all their personality and memories dissolving in it (which is what tends to happen to people forcibly connected to an element without an additional tether like that, sometimes reversibly and sometimes not). Nika and Kira are both in the domain of the Fox, while Hana is in the domain of the Rabbit. Fox is more proactive and generally benevolent, but can get them in trouble that requires Hana, backed by her more passive and disinterested (less helpful but also less obstructive) patron, to pull them out of.
Fox is the one that manifests as their ‘mentor’ at the very beginning, although she loses interest / forgets about them / gets distracted fairly frequently, so they still have to find their own path for the most part. It actually takes a lot of time before the girls even learn that Rabbit exists, much less has any kind of connection to their team (Fox neglects to explain that, along with many other things she deems irrelevant / inconvenient / funnier if they don’t know).
Yes, Kira’s hair really IS that color. People tend to assume she dyes it (yes, she’s like 12, but it just fits really naturally as an assumption about her that she would), but actually she doesn’t, it’s just a severe case of Protagonist Syndrome (no thanks to Fox’s sense of humor). Even though she’s, uh, not the actual protagonist, that’d be Nika XD
The setting is a fictional world in which magic / deities and spirits are marginally more known about, but the girls still maintain secret identities. Part of the reason is that the very first fight ends with their opponent promising to track them down and make their lives hell; part is that they aren’t crazy about the idea of taking responsibility for all the collateral damage (sure, they eventually get the hang of minimizing and mending it, but not immediately, and there’s always still some left). Hana’s powers are definitely immediately helpful with the secret identities, yes. Nevertheless, their parents figure it out fairly fast, but as they’re literally backed/guided by deities, don’t try to stop them. Hana’s pretend nothing is happening, Kira’s just take it in stride like ‘we always knew something like this was going to happen, she’s Just Like That’, and Nika’s try their best to be supportive and helpful, even if they take their time revealing that actually yeah they do know about her big secret).
5 notes · View notes
isiyasy · 5 years
Quote
Haka dai Husaini (a.s) ya ci gaba da ganawa da Ubangijinsa a daidai wannan lokaci alhali kuwa sojojin abokan gaba sai dada gabatowa suke yi. Tun kafin haka dai, Husaini (a.s) ya shirya sansaninsa inda ya tona rami a bayansa da kuma sanya wuta cikin ramin don hana abokan gaba bullo musu ta baya da kuma kare mata da kananan yara daga hare-haren abokan gaban. Lokacin da Shimr ya ga wannan wuta da take ci fal-fal, sai ya yi ihu ya ce: "Ya Husaini, shin kana gaggawan shiga wuta ne tun kafin Ranar Kiyama?, sai Imam Husain (a.s) ya amsa masa da cewa: "Kai ne ka fi cancanta da shiga cikinta". Jin wannan kalami ya Shimr ya sa daya daga cikin sahabban Husaini (a.s) wato Muslim bn Awsaja ya yi kokarin harbo shi da kibiya, to amma sai Husaini (a.s) ya hana shi yana mai cewa: "Kada ka harbo shi don ba na son ya kasance ni na fara kai musu hari". Wannan dai shi ne irin kyakkyawan hali na Musulunci yayin yaki, wannan kuma shi ne irin dabi'un shugaban shahidai al-Husaini (a.s) wanda babu yadda za a yi ya kauce wa hakan ko da kuwa wani irin mummunan hali ya ke ciki. Duk kuwa da irin wannan dabi'a ta kwarai gare shi, to amma wannan la'ananne Shimr bn Zil Jawshan shi ne wanda zai kashe Husaini (a.s) bayan dan wani lokaci a wannan rana. Kafin fara wannan yaki dai, a matsayin kafa hujja ga wadannan sojoji na Yazid bn Mu'awiyya, Imam Husain (a.s) ya bukace su da su yi shiru don ya gabatar musu da wani jawabi, to sai dai sun ki amincewa da hakan suna masu sake daga muryoyinsu, to amma dai daga karshe sun yarda su yi shirun don sauraronsa. A nan Husaini (a.s) ya tunasar da su gayyatar da suka masa da kuma wasikun da suka aika masa suna kiransa da ya zo ya jagorance su, kamar yadda kuma ya sanar da su abin da zai faru gare su ta hannun wadannan azzalumai da suka turo su wato sarakunan Umayyawa, kamar yadda kakansa (s.a.w.a) da kuma babansa (a.s) suka sanar da shi, hakan kuwa ya faru. Sannan kuma ya sanar da jagoran wadannan dakaru Umar bn Sa'ad cewa lalle fa alkawarin da aka masa na ba shi garin Ray ba za a cika shi ba, kuma lalle za a kashe shi da kuma tsire kansa a kan mashi.  Wasu daga cikin sahabban Imam Husain (a.s) irin su Zuhair bn al-Kain da Burair bn Khudhyar sun yi kokarin yin bayani ga wadannan sojoji yadda lamari yake da kuma dalilan wannan yunkuri na Husaini (a.s) to amma ina sun ki su saurare su da kunnen basira. Daga nan Husaini (a.s) ya sake dawowa gaban wadannan sojoji na abokan gaba yana mai ce musu: "Bayan haka, ku duba da kyau ku ga ko ni wane ne sannan ku koma ga zukatanku ku tambayesu shin ya halalta gare ku ku kashe ni da kuma keta mutumcina? Ashe ni ba dan 'yar Manzonku (s.a.w.a) ba ne kuma dan wasiyyinsa kuma dan baffansa, wanda ya fara imani da Allah da kuma gaskata ManzonSa ba? Ashe Hamza shugaban shahidai ba baffan babana ba ne? Ashe Ja'afar al-Tayyar ba baffana ba ne? Ashe kalamin Manzon Allah (s) dangane da ni da dan'uwana bai iso gare ku ba, inda yake cewa: 'Wadannan guda biyu su ne shuwagabannin samarukan aljanna? To idan har kun gaskata ni kan abin da na ce - kuma hakan ita ce gaskiya- wallahi ban taba ganganta yin karya ba tun daga lokacin da na san cewa Allah zai azabtar da ma'abucinta. Idan kuwa kun karyata ni to cikinku akwai wanda idan kuka tambaya shi kan hakan zai gaya muku, ku tambayi Jabir bn Abdullah al-Ansari, ko kuma Abu Sa'id al-Khudri ko kuma Sahl bn Sa'ad al-Sa'idi, ko kuma Zaid bn Arkam ko kuma Anas bn Malik , za su tabbatar muku lalle sun ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana fadin wannan zance a kaina da dan'uwana. Ashe wannan ba zai kasance muku shamaki wajen zubar da jinina ba? Sai Husaini (a.s) ya ci gaba da cewa: "Idan har kuna shakku ne kan wannan abin da na fadi ko kuma kan cewa ni dan 'yar Manzonku ne, to wallahi babu wani dan 'yar Annabi a bayan kasa daga cikinku ko kuma da cikin wasunku in ba ni ba. Ni ne kawai dan 'yar Manzonku, ku gaya min shin kuna neman fansar jinin wani ne da na kashe daga cikinku? Ko kuma wata dukiya taku da na cinye? Ko kuma fansar wata cuta da na yi wa wani(1)?. Babu dai wani da ya amsa masa, don haka sai ya ci gaba: "Ashe ba ku ga takobin Manzon Allah (s.a.w.a) a tare da ni da kuma rawaninsa a kaina ba? Sai suka ce: "Na'am", sai ya ce musu: "To kada ku yake ni", to amma ina ba su amsa masa ba face sai da amsar da bawan da ba shi da wani iko ko karfi na kansa zai amsa wa ubangijinsa, wato sai suka ce: "Mu masu biyayya ne ga sarki Ubaidullah bn Ziyad(2), daga nan sai ya ce: "Wallahi ba za ku dade a duniya ba sama da lokacin da ake bukata wajen hawa kan doki, kafin duniya ta yi wasan kura da ku kamar yadda dutsen nika da kuma jujjuya ku kamar maratayi. Hakika wannan shi ne abin da babana ya gaya min yana mai nakaltowa daga kakana Manzon Allah (s.a.w.a). Don haka sai ku tara al'amarinku, ku da abubuwan shirkanku, sa'an nan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri. Hakika, ni na dogara ga Allah, Ubangijina kuma Ubangijinku. Babu wata dabba face Shi ne Mai riko da kwarkwadarta. Hakika Ubangijina Yana (umurni) a tafarki madaidaici(3)". Duk wannan abin da ake yi kuwa Umar bn Sa'ad yana nan a kan bakansa na yakan Husaini (a.s), duk kuwa da cewa ya yi kokarin janyo hankalinsa da kada ya zubar da jininsa, amma a banza, don haka sai ya dube shi ya ce masa: "Ya Umar, shin kana tunanin za ka kashe ni wannan mutumin banzan ya ba ka sarautar Ray da Gorgan ne ko, to wallahi ba za ka samu hakan ba, don kuwa hakan wani al'amari ne da aka riga aka rubuta shi. Don haka ka aikata abin da kake son aikatawa, lalle kuwa ba za ka taba zama cikin farin ciki da kwanciyar hankali ba bayana, a nan duniya ne ko kuma a lahira. Lalle ina mai ganin kanka yaran Kufa suna wasa da shi(4)". Nan take sai Shaidan ya yi galaba akan Ibn Sa'ad, inda ya kira wani sojansa: "Ya Duraid kawo tutarka", daga nan sai ya sa kibiyarsa ciki baka ya harba cikin rundunar Imam Husain (a.s) yana mai cewa: "Kowa ya shaida ni ne na farko da na fara harbawa", daga nan sai aka fara ruwan kibau tsakanin sojojin biyu da kuma fada da juna(5). Ta haka ne dai Ibn Sa'ad ya kunna wutan wannan yaki ta hanyar harba kibiyarsa cikin tantin Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) mutanensa su ma suka biyo sahu suka ci gaba da ruwan kibau a kan Husaini (a.s) da mabiyansa, ta yadda babu wani daga cikin sahabbansa da kibiya ba ta same shi ba. Wannan lamari dai mai girma ne ga Imam Husain (a.s) don haka sai ya juya kan sahabbansa yana mai ce musu: "Ku mike - Allah Ya yi muku rahama - don fuskantar mutuwar da babu makawa gare ta, don kuwa wadannan kibau manzannin wadannan mutane ne gare ku(6)". Duk da cewa dakarun Imam Husain (a.s) ba su da yawa idan ka kwatanta su da dubban sojojin abokan gaba, amma hakan bai sanya komai kashin rauni ba cikin zukatan sahabban Husaini (a.s), babu wani babba ko karami daga cikinsu da ya ja da baya, face ma dai dukkansu suka amsa wannan kira na shugabansu Husaini (a.s) inda suka fuskanci abokan gaba da dukkan karfinsu kamar zakin da ya ga babban abokin gabansa. Haka dai aka ci gaba da gumurzu tsakanin bangarorin biyu, kura ta turnuke wuri ya cakude har na tsawon kimanin awa guda, daga nan bayan da kura ta lafa, sai ga sahabban Husaini guda hamsin sun yi shahada(7). Daga nan sai wasu daga cikin mutanen Umar bn Sa'ad suka bukaci sahabban Husaini (a.s) da su fito a kara, inda nan take Habib bn Muzahir, Burair da Abdullah bn Umair al-Kalabi suka bukaci Imam Husain (a.s) da ya ba su izinin fita don rige-rigen samun darajar shahada. Imam Husain (a.s) ya amincewa Abdullah da ya fita zuwa filin daga da shahada, ba tare da bata lokaci ba kuwa ya fito fili. Lokacin fitarsa sai matarsa Umm Wahab ta kalle shi sai ta ga jini na zuba a hannunsa saboda raunin da ya samu, wannan yanayi ya motsa mata rai, sai ta ballo daya daga cikin sandunan tanti ta nufo inda mijinta yake tana ce masa: 'Mahaifana su kasance fansa gare ka zan yi fada don kare zuriyar Manzon Allah (s.a.w.a)', sai mijin nata ya yi kokarin komar da ita inda mata suke, amma sai ta kama tufafinsa tana cewa: 'Lalle ni ba zan koma ba har sai dai in mutu tare da kai'. Ganin haka sai Husaini (a.s) ya kira ta ya ce mata: "Allah Ya saka miki da alherinSa a madadin Iyalan Gidan Annabinku, koma cikin tanti don ba a wajabta wa mata yaki ba(8)". Haka dai yakin ya ci gaba a Karbala, jini mai tsarki na sahabban Imam Husaini (a.s) ya ci gaba da zuba da gudana zuwa makoma, kamar yadda daya bayan daya suka ci gaba da faduwa kasa da yin shahada. To sai dai kuma ba wai haka kawai suka faduwa din ba, don kuwa su ma sun kashe da kuma raunana da dama daga cikin sojojin Umayyawan, ganin haka ne ma ya sa Umar bn Sa'ad ya umarci sojojin nasa da kada su yarda da yin yaki gaba da gaba da sahabban Husaini (a.s), face dai kawai su dinga kai musu hare-hare na gaba daya da taron dangi da kuma amfani da dukkan makaman da suke hannunsu. Don haka sai wata tawaga ta sojojin Umayyawan karkashin jagorancin Amru bn al-Hajjaj, suka zaburo wa dakarun Imam Husaini (a.s) marasa yawa ta bangaren dama, lamarin da ya tilasta wa wasu daga cikin sojojin Imam Husaini (a.s) tsayin daka da kuma fuskantar abokan gaban da masunsu, wannan lamari dai ya amfanar don kuwa ya taimaka wajen mayar da dakarun Umayyawan baya da kuma ba wa sahabban Husaini (a.s) ci gaba da harba kibau a kan wadannan sojojin. Har ila yau kuma wasu dakarun abokan gaban karkashin jagorancin Shimr su ma suka kawo nasu harin ta bangaren hagu na sansanin Imam Husaini (a.s), a nan ma dai sojojin Husaini (a.s) din sun nuna gagarumar jaruntaka, inda suka sami nasarar fatattakan Shimr da dakarunsa. A yayin wannan gumurzu dai jarumin sahabin nan na Husaini (a.s) wato Abdullah bn Umayr al-Kalbi ya nuna jaruntaka inda ya kashe sojoji mahaya na abokan gaba 19 da kuma wasu guda 12 na sojojin kafa, kafin su ci karfinsa su kama shi su kashe shi. Matarsa Umm Wahab ganin abin da ya samu mijinta, sai ta gagara jurewa, inda ta nufi filin dagan da kuma faduwa wajen gawar mijin nata mai tsarki tana ce masa: 'Barka gare ka da samun Aljanna. Ganin irin wannan jarunta ta wannan baiwar Allah, sai Shimr ya umarci daya daga cikin sojojinsa da ya kashe ta, sai ya sanya wani karfe ya bugi kanta da kuma yanke shi gaba daya, inda ya fado cikin sansanin Imam Husaini (a.s), ta fadi a matsayin shahida. Irin wadannan hare-hare da sojojin abokan gaban suke kai wa ya tsananta, don kuwa kusan sun zagaye Husaini da Sahabbansa ne (a.s), wannan dai ya ba wa wasu daga cikin sojojin Umayyawa daman shiga har cikin tantunan mabiya Husaini (a.s) da kuma sace wasu kayayyaki da suke da shi. Daga nan kuma sai Umar bn Sa'ad ya ba da umarni wa sojojin nasa da su sa wuta wa tantunan, lamarin da ya tilasta wa yara da mata da suke cikin tantunan fitowa cikin dimautuwa da halin mai ban tausayi. Duk da cewa dai a daidai wannan lokaci rana ta kai tsakiya ga ta da kunar gaske, a waje guda kuma ga tantunan Iyalan gidan Manzo (s.a.w.a) suna cin wuta to amma duk da haka ba abu ne da za a iya tunaninsa ba ma cewa Imam Husaini (a.s) zai mance da batun salla. Ko da ya lura da cewa lokacin salla ya yi, sai ya umarci mabiyansa da su hadu don sauke farali, to sai dai kuma saboda yanayin da suke ciki na yaki ba su sami damar tsayawa sosai da ganawa da Ubangijin nasu ba(9), bayan sun idar da salla kuma sai suka dawo fagen fama, inda suka ci gaba da gumurzu da abokan gaban, daya bayan daya na fita amma ba tare da dawowa ba: babban dansa Ali al-Akbar; 'yan'uwansa Ubaidullah, Uthman, Ja'afar da Muhammad; 'ya'yan dan'uwansa Imam Hasan: Abubakar da Al-Kasim da al-Hasan al-Muthanna (na biyu)(10); dan kanwarsa Zainab: Awn bn Abdullah bn Ja'afar al-Tayyar; iyalan Akil: Abdullah bn Muslim bn Akil da Abdurrahman bn Akil da Ja'afar bn Akil da Muhammad bn Muslim bn Akil da Abdullah bn Akil. A daidai wannan lokaci dai wadannan jaruman iyalai na gidan Akil da Aliyu bn Abi Talib (a.s) duk sun kasance shahidai, jikkunansu masu tsarki kuwa suna nan zube a wannan fili na daga kamar wasu taurari masu haske da haskakawa. Imam Husaini (a.s) dai ya tsaya a gaban wadannan shahidai yana mai sane da cewa nan ba da jimawa ba zai biyo su, sai dai kuma yana cikin damuwa saboda kukan da kananan yara da mata suke yi saboda abubuwan da suke gani. Wannan lamari ya sanya Imam Husaini (a.s) ya fara neman wani mai taimako, inda yake cewa: "Shin akwai wani mai taimako da zai taimaka wa matayen gidan Manzon Allah (s.a.w.a)? Shin akwai wani mai imani da tsoron Allah da zai taimake mu? Shin akwai wani mai taimako dake neman sakamakon Allah don ya taimaka mana(11)?. Amma ina babu wanda ya amsa masa face kukan mata da kananan yara, lamarin da ya sanya Imam Husaini (a.s) ya yanke kauna sannan kuma ya san cewa babu wani abin da ya saura masa in ban da fuskantar abokan gaba. A daidai wannan lokaci dai zuciyarsa cike take da tausayawa ga kananan yaran da suke cikin tantuna bugu da kari kan tausayawa irin ta Uba ga dansa Abdullah wanda zai bar shi don ya san ba zai dawo ba daga fitan da zai yi. Don haka sai ya tafi tantin kanwarsa Zainab, ya bukace ta da ta kawo masa wannan da nasa don ya sumbance shi da kuma ganinsa a karo na karshe. Nan take Zainab ta shiga ta kawo shi, ko da ya yi kokarin sumbantar lebbansa sai ya ji lebban a bushe kamar ita ce saboda tsananin kishirwan da ya ke damunsa. To amma a daidai wannnan lokaci sai ga kifiya nan daga sansanin abokan gaba ta shigo ta gutsure dan makogwaron wannan jariri(12) da kuma raba shi da rayuwa. Ta haka ne wannan jariri ya rubuta sunansa da wannan jini nasa mai tsarki cikin tarihin irin musiba da zaluncin da ya samu Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) ranar Ashura a Karbala. A irin wannan hali mai ya kamata Husaini (a.s) ya aikata? Ya ya ake tsammanin Uban da ke cikin wannan hali na gudanar jinin jaririn dansa mai shan nono wanda yake kallonsa yana masa murmushi? Me ake tsammanin Husaini (a.s) zai aikata a lokacin da ya ke ganin an kashe masa wannan jaririn da? Haka dai Husaini (a.s) ya tsaya kamar wani dutse, wannan lamari dai bai raunana shi ko kuma jin juyawa da baya ba, face dai sai ya tara dan jinin da ya fito daga makogwaron jaririn ya daga sama yana mai isar da kukansa ga Allah Madaukakin Sarki, yana cewa: "Ina cikin kwanciyar hankali ganin cewa Allah Madaukakin Sarki yana ganin wannan hali da nake ciki(13)". Da haka ne jini ya fara gudana a kasar Karbala kana kuma wannan babban bala'i ya fara daukan ainihin yanayinsa na hakika, bugu da kari kan tsananin kishirwa da ya zamanto yana damun mata da yara da suke cikin tantunan sansanin Imam Husain (a.s). Ganin haka sai Imam Husain (a.s) ya hau dokinsa dan'uwansa Abbas (a.s) na gaba gare shi suka nufi kogin Furat da nufin samo ruwa wa wadannan iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) da suka saura wadanda kuma suke cikin mawuyacin hali da rashin ruwa. To sai dai kuma sojojin abokan gaba sun taso musu inda suka raba tsakaninsu, Husaini (a.s) yana wannan sashi, shi kuma Abbas (a.s) yana wancan. A daidai wannan lokaci sai Abbas ya fuskanci sojojin abokan gaba inda ya zubar da na zubarwa da kuma raunana na raunanawa, har lokacin da suka samu nasara a kansa suka raunana shi(14), jinin shahada na zuba masa amma dai yana rike da tutan Husaini (a.s) tabbatacciya wacce za ta ci gaba da tabbatuwa har ranar karshe da kuma jijjiga daulolin ja'iran shuwagabanni. A daya bangaren kuma Husaini (a.s) ne yake ta kokarin isa zuwa ga wannan kogi na Furat don debo ruwan, to sai dai kuma wata bataliya ta sojojin abokan gaba sun hana shi isa, inda wani daga cikin sojojin Ibn Sa'ad ya harbo kibiyarsa zuwa gare shi inda ta same saman bakinsa, ko da Husaini (a.s) ya cire wannan makami sai jini ke fitowa, sai ya tara wannan jini da watsa shi sama yana mai bayyana wa Ubangijinsa cewa: "Ya Allah ina isar da kuka gare Ka kan abin da aka yi wa dan 'yar AnnabinKa(15)". Ta haka ne dai wannan fili na Karbala ya cika da shahidai da wadanda aka raunana daga cikin Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) da kuma sauran bayin Allah da suka ba da rayukansu don tabbatar da wannan addini da kuma share wa al'ummomi fagen yunkuri da jihadi. Imam Husain (a.s) ya duba ko ina ya ga babu wani daga cikin sahabbai ko kuma iyalansa face yana kwance cikin jinin shahada, daga nan sai ya sake rera wadannan baitoci na waka: Zan tafi don mutuwa ba abin kunya ba ne ga matashi,               Lokacin da ya so gaskiya da yin jihadi kamar musulmi. Wanda ya so salihan mutane ta sadaukar da kansa,               To ya rabu da la'anannu da kuma saba wa mujirimai. In na rayu zan yi nadama, in na mutu ba za a zargeni ba, Ya ishe ka wulakanci, zama cikin rashin nitsuwa. Don haka a halin yanzu dai ga Husaini (a.s) nan shi kadai yana dauke da takobin Manzon Allah (s.a.w.a), a waje guda kuma ga zuciyar Ali (a.s) a hannunsa kuma ga tutar gaskiya, a harshensa kuma ga kalmomin tsoron Allah. Ya tsaya a gaban wadannan sojoji wadanda shaidan ya riga ya saye su, ba abin da suke tunani in ban da kashe Imam Husain (a.s) da kuma yin sukuwa a kan jikinsa mai tsarki. Wannan rana dai ita ce ranar da Manzon Allah (s.a.w.a) ya ba shi labarinta kuma wannan dai shi ne abin da aka yi masa alkawari da shi. Daga nan sai Husaini (a.s) ya sabi takobinsa, ya nufi sansanin abokan gaba yana mai kirari kamar dai yadda al'adar yaki take. Abokan gaba su ma suka nufo shi suna sara yana yi, ta yadda babu wani wanda zai fuskanto shi face sai ya kwantar da shi da kuma tura shi Jahannama cikin wulakanci. A daidai lokacin da Husaini (a.s) yake wannan yaki kuwa, zuciyarsa kuma tana komawa zuwa ga tantunan mata da yara da suka saura daga cikin mabiyansa. Loka-cin da ya ga Umar bn Sa'ad da mabiyansa sun raba tsaka-ninsa da sansaninsa kuma suna kokarin kai wa mata da yara hari, sai ya yi musu tsawa da cewa: "Ni ne nake yaki da ku, mata ba su da wani laifi, don haka ka hana wadannan mugayen sojoji naka daga keta hurumina matukar ina raye(16)". Amma ina! wadannan kalmomi na dan 'yar Manzon Allah (s.a.w.a) ba su yi wani tasiri a zukatan wadannan azzalumai ba, maimakon haka ma sai Shimr bn Zil Jawshan tare da wasu sojojinsa suka nufi inda wadannan iyalai na Husaini (a.s) suke, ganin haka sai ya yi musu tsawa yana mai cewa: "Kaiconku! Idan har ba ku da addini kana kuma ba kwa jin tsoron ranar Kiyama, to alal akalla ku zamanto 'yantattu masu tunani mana, ku nisanci cutar da iyalaina". Sai Ibn Zil Jawshan ya ce: "Wannan shi ne abin da ya dace da kai Ya kai dan Fatima". Haka dai wadannan hare-hare masu tsanani suka ci gaba, Husaini (a.s) kuma yana nan a tsakiyar wadannan sojoji marasa imani da tausayi, har lokacin da daya daga cikin sojojin ya harbo kifiyarsa zuwa ga Husaini (a.s) inda ta same shi a makogwaro. A bangare guda kuma sauran sojojin sai ruwan kibau, takubba da masu suke wa Imam Husain (a.s), har lokacin da ya kai ma ba ya iya wani abu na fuskantar abokan gaban saboda yawan raunukan da ya samu a jikinsa mai tsarki jini kuwa ta ko ta ina sai zuba yake yi yana rubuta irin jaruntar da ya yi a wannan rana da kuma irin zaluncin da tarihi bai taba ganin irinsa ba da aka yi masa da iyalai da kuma sahabbansa. Wadannan raunuka guda sittin da bakwai(17) da suke jikinsa sun kasance wata alama ce mai magana da ke nuni da tsayin daka, jihadi da kuma irin zaluncin da aka masa. Haka nan Husaini (a.s) ya fadi, yana jan jikinsa mai tsarki dake cike da jini don tafiya wani waje da zai buya daga idanuwan iyalansa da suke cikin mawuyacin hali, to sai dai kuma duk wannan yanayi mai ban tausayi da sosa rai bai sanya zukatan wadannan mutane da suke cike da gaba da kiyayya sun dan sassauto ba, face ma dai sai Shimr bn Zil Jawshan ya nufi inda Husain din yake dauke da takobinsa na zalunci, don sare daya daga cikin rassan bishiyar annabci. Don ya yanke kan daga jikin da kuma kai wa dagutu a matsayin kyauta yana mai jiran shi kuma a saka masa da abin duniya, wannan kai da duk tsawon tarihi yana sujada wa Allah, da kuma harshen da a ko da yaushe yake ambaton Allah. Wannan harshe da yake nanata wannan jumla: "Wallahi ba zan taba mika muku hannuna ba a matsayin mutum wulakantacce, kamar yadda kuma ba zan yi ikirari kamar ikirarin bayi ba". Wannan kai dai da ke cike da daukaka wanda kuma ya ki yarda ya mika wuya ga dagutu ko kuma ya hada kai da azzalumai ba. Haka dai ya yanke wannan kai mai tsarki da daukaka da raba shi da asalin jiki mai tsarki. Haka dai wannan aika-aika ya auku, haka kuma aka kashe Husaini (a.s) tare da sauran mabiyansa madaukaka, da kuma daukan wannan kai da wucewa da shi, kafin dai a dawo da shi, bayan an kai shi Kufa da kuma Sham, zuwa Karbala a bisne shi a gefen wannan jiki mai tsarki. ____________ (1)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 322 da 323 da kuma Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 61 da 62. (2)- Maktal al-Husain na Abdurrazak al-Mukarram, shafi na 233 da 234. (3)- Maktal al-Husain na Abdurrazak al-Mukarram, shafi na 235. (4)- Lalle Imam Husain (a.s) ya yi gaskiya don kuwa Umar bn Sa'ad bai sami komai ba in banda bakin ciki da wulakanci, bayan da Mukhtar bn Ubaidah al-Thakafi ya kashe shi a garin Kufa, Dubi littafin Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 241. (5)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 236. (6)- Maktal al-Husain na Abdurrazak al-Mukarram, shafi na 237. (7) - Kamar na sama (8)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 327 da al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 65. (9)- An ruwaito cewa Imam Husaini (a.s) tare da sahabbansa sun yi sallar ne ta hanyar ishara saboda rashin samun damar yin sallar kamar yadda suka saba kuma sun yi sallar tsoro ne. Wannan labari dai Dabari ya ruwaito shi cikin Tarikh al-Umam wa al-Muluk, juzu'i na 4, shafi na 334 da kuma Ibn Athir cikin Al-Kamil fi al-Tarikh juzu'i na 4, shafi na 69. (10)- Hasan al-Muthanna dai ya samu raunuka ne da yawa amma dai bai yi shahada ba, an dauke da kuma yi masa magani. (11)- Maktal al-Husain na Ibn Dawus, shafi na 49. (12)- Mutumin da ya harbo wannan kifiya kuwa shi ne Harmala bn Kahil, kuma malaman tarihi sun ce shahadar wannan jariri Abullah ta zo kafin shahadar baffansa Abbas, lokacin da babansa ya bukaci abokan gaban da su taimaka wa yaron da ruwa don ya sha, amma maimakon ruwan sai suka harbo kibiyar da ta kashe shi. (13)- Maktal al-Husain na Sayyid Ibn Dawus, shafi na 49, haka nan ma Dabari cikin Tarikh al-Umam wa al-Muluk ya kawo wannan labari cikin juzu'i na 4, shafi na 342 da kuma Ibn Athir, juzu'i na 8, shafi na 187. (14)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 240. Abbas dai kani yake wa Imam Husain (a.s) ta wajen mahaifinsa, mahaifiyarsa kuwa ita ce Ummul Banin Fatima 'yar Hizam al-Kalbi. (15)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 240. (16)- Maktal al-Husain (a.s) na Ibn Dawus, shafi na 50. (17)- Suka talatin da uku aka yi wa Imam Husain (a.s) da mashi, sannan saran takobi kuma talatin da hudu, kamar yadda ya zo cikin Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 344-346.
http://www.5five-stars.com.ng/2019/09/dawwa-mammen-yaki.html
0 notes
lilietsblog · 6 years
Photo
Tumblr media Tumblr media
side to side comparison
okay so maybe Kira’s hair color is kind of conspicuous but
1 note · View note
lilietsblog · 6 years
Photo
Tumblr media
Hana, Kira and Nika in their civilian identities, aka Yep People Don’t Recognize Them