Tumgik
#kyamar
hippieinhills · 2 years
Photo
Tumblr media
The Rumtse to Tsomoriri Trek 2023 One of the most beautiful hiking adventures in the region of Ladakh. A high altitude trek which takes you through the spectacular Changthang region home to Changpa nomads and their hundreds of Pashmina goat and yaks. An exceptional trek going through numerous high Passes above 5000m. Plan this hiking trail as your next mountain adventure for the season. If you would like to join a group, check for our fixed departure dates. . . #rumtsetsomoriritrek #rumtsetotsomoriri #rumtsetotsomoriritrek #rumtsetokorzok #rumtsetsomoriri #tsokar #rumtse #tsomoriri #changthang #changpa #landscape #kyamar #mandalchanla #doksa #yalungnyaula #hikingadventures #remotetreks #trekkinginladakh #trekkinginchangthang #rupshu #trekkinginindia #trekkinginindianhimalayas #trekwithhippieinhills #trekwithlocals #adventurasindia #himalayantreks #dekhoapnadesh #hippieinhills #ladakh (at Ladakh, India) https://www.instagram.com/p/CqFFACSJO-b/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
isausmanmohd · 2 years
Photo
Tumblr media
KA GIRMAMA KOWA, AMMA KA RIBANYA GIRMAMAWARKA GA "MAHAIFIYA" Babin rayuwar kowa yayin gagwarmayar kaiwa zuwa ga nasara cike yake da kadaici, tsangwama, hantara,kyama da kuma kalubale daga dukkanin kusurwowi, amma babin farko na samun nasarar kowa, mutane zasu dinga ketowa. Martabawa, girmamawa da soyayya shine abinda zai ke bayyana a tattare da su gareka. Ashe dai a hakika mutane ba suna ki ko kyamatar zatin mutane ba ne, ba kuma suna girmamawa ko kaunar zatin mutane ba ne, suna ki da kyamar duhun dake tattare da su ne, sannan kuma suna zumudin son amfana da hasken dake tattare da su ne.( Wato soyayyarsu gareka dalilinta haskenka, kyamarsu gareka dalilinsa duhunka). Amma ita Mahaifiya itace take cike gibin dake a tsakani na sanin kimar zatinka, soyayyarta gareka sam ya girmi ajin dalili, tun daga busa numfashin ka na farko, burinta ta haskaka rayuwarka da hasken kauna dake fitowa cikin zuciyarta, bata san duhunka ba, balle sadda ka riski haske wani abinka ya rudeta, kuma ba ta da ranar da zata daina kaunarka, ko kuma ta gujeka saboda wani abinda kake tattare da shi ya kubce maka. Mai yiwuwa shi yasa ko a hadisi yazo, ko da mai tambaya ya tambayi ANNABI (S.A.W) Shin wa zai yiwa biyayya akan kowa, Sai yace da shi "Mahaifiya" yana fadi yana nanatawa kafin ya ambaci waninta. (Muhammad Usman Gashua✍️) YA ALLAH KA TSAREMU SABAWA IYAYE, KA BAMU IKON SANYAYA DUBANSU GAREMU. ALHAMDULILLAH. (at Nigeria) https://www.instagram.com/p/Cp_D2uFoMSM/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
indiapictures · 5 years
Photo
Tumblr media
Trans Himalaya 2019 update. Crossed 111 passes in 111 days so far over 2500km and 150 thousand meters elevation gain across Uttarakhand, Himachal, Ladakh, Zanskar, Lahaul. Photo shown here crossing the 100th pass, the Gotunte La at 5150m in remote Zanskar above the Tsarap river valley. . Truncated... C. Ladakh. . P54. Namste La 4490m P55. Namste La (2) P56. Parfi La 3900m P57. Hanuma La 4730m P58. Netuke La 4380m P59. Kyupka La 4440m P60. Singge La 4950m P61. Sirsir La 4800m P62. Nigutste La 5100m P63. Yogma La 4720m P64. Prinkti La 3700m P65. Konski La 4900m P66. Lanak La 4100m P67. Dungduchen La 4600m P68. Zalung Karpo La 5170m P69. Yar la 4940m P70. Pogmar La 4980m P71. Shingbuk La 5280m P72. Mandalchan La 5210m P73. Kyamar La 5100 P74. Shapodak la 4660m P75. Shang La 4930m P76. Matho La 4950m P77. Stok Kangri 6140m P78. Stok La 4846m P79. Ganda La 4960m P80. Stakspi / Sminopi La 5150m P81. Mangyu La 4150 P82. Ipti La 4130m P83. Tar La 4900m D. Zanskar, Ladakh P84. Prinkti La 3700m P85. Yogma La 4740m P86. Kanji la 5240m P85. Yogma La 4740m P86. Kanji la 5240m P87. Pidong la 5020m P88. Barmai la 4670m P89. Netuke La 4430m P90. Kyupka La 4400m P91. Kong la 3940m P92. Chochogori La 3960m // Deadend at Nerak, U turn P93. Chochogori La x 2 P94. Kong La x 2 P95. Kyupka La x 3 P96. Netuke La x 3 P97. Hanuma La x 2 P98. Parfi La x 2 P99. Niala Konste La 4830m P100. Gotunte La 5140m P101. Tsarap I pass 4360m P102. Tsarap II pass 4380m P103. Marang La 5350m P104. Jinzby La 4620m P105. Pogmar La x 2 P104. Jinzby La 4620m P105. Pogmar La x 2 P106. Tsarap II pass x 2 P107. Tsarap I pass x 2 Heavy rains / early snowfall blocked route P108. Tsarap I pass x 3 P109. Tsarap II pass x 3 P110. Rangcha Gali 4413m P111. Beas Kund 4700m. . Credits: @petervangeit. . #himalayas #trekking #india #himalayanpass #mountainpass #wanderlust #nature #leh #ladakh #indiapictures #indicrew @indicrewexpeditions https://ift.tt/2ZinItW
0 notes
hausafilmstv · 5 years
Text
Gwamna Matawalle Na Jihar Zamfara Ya Gaisa Da Kuturu
INUWA BA KI KYAMAR KOWA
Allah Sarki Gwamnan da ba ya kyamar al'umma. Idan mai karatu ya lura, a nan Gwamnan jihar Zamfara ne yake gaisawa da wani Bawan Allah wanda Allah ya jarabta da cutar kuturta. Inda suke gaisawa bisa girmamawa da darajawa.
cigaba da karatu » from Hutudole: labarai da hausa https://ift.tt/36QY5pe via https://ift.tt/2whmJRK
0 notes
nasurumaikwano · 5 years
Text
Na dade ina son yin sharhi a kan maganar AUREN TAZARAN SHEKARU.
Sai yau Allah Ya bani iko.
Ina fatar makaranta rubutu na zasu yi dogon tunani, tare da lissafi na GASKIYA da wannan alamarin.
Da yake har yanzu Alummah ta tana wa wannan irin AURE kallon WAUTA, ko aure na wanda mai yin shi yana da BUDURWAN ZUCIYA ko wani BUKATA daban da ya wuce yi SABODA DA ALLAH ko KAUNA ko ma TAUSAYI, har yanzu irin wannan auren kusan a CAMFE yake.
Tambaya a nan shi ne, ko yaushe zamu kawar da wannan JAHILCI daga zukatan mu don alummahn mu ta samu natsuwa oho?
E, ta samu natsuwa mana....domin har yanzu mutane suna TSORON auren tazaran shekaru in da MACE ta girmi namiji ko NAMIJI ya girmi mace...amma musamman in da mace ta fi shekarun.
Duk da yake mu yawancin mu musulmai ne, mun kuma karanta cewan Annabi SAW yayi irin wannan tazaran auren tun farkon auren shi, inda matar shi Khadija ta zamanto wadda ta girme shi, nesa ba kusa ba, kuma ta fi shi KUDI, mun kasa natsuwan da yakamata a irin wannan auren.
Duk da wasu da yawa sukan yi TAURIN KAN rashin mutunta wannan batu, kuma su hada da cewan su ba annabawa bane, ai basu musunta sauran abubuwan da yayi irin su jihadi, aje gemu da hajji da umrah da sauransu.
Watau idan kun lura, YAWANCIN 'YAN ADAM suna da wani GIRMAN KAI da RASHIN SON aci arzikin su kai tsaye, da kuma cewan idan ba zasu iya wani abu ba, wani ma ba zai iya ba!
Har da kuma cewan idan ba sa son abu, ko magana bai masu daidai ba duk GASKIYAR da ke cikinta ba zasu yarda ba.
Tabbas an fi zaton namiji ya auri wadda ya girma kamar yadda Annabi Yayi da Aisha, wanda duka Allah Ya Hukunta don muyi koyi, amma ba'a cika amincewa da na mace ta girmi namiji ba.
Wai wasu sunce saboda kula da sauransu, bayan kusan ko wace mace a yau tana fafikan kula da kan ta, auren ne kawai babu.
Abin haushi shi ne saboda KETA, da rashin son SADAUKARWAR wasu matan, sun jin asaran mai auren su yaci arzikin su duk da sayen ALJANNA da arzikisu yafi masu ajewa a gada.
Wai a ganin su za'a yi masu WAYO, bayan rashin wayo bai wuce su mutu ta bar kudin da ba sa so su sadaukar ba!
Abin da ke da ban takaici kuma shi ne, har yanzu maza da mata suna matukar wulakanta maganan mace ta auri wadda ta girma ko da da shekara daya ko biyu ne balle fiye.
Toh!
Allah YaCe DAI DAI ne.
Ance abin yayi bambarakwai!
Ance yin hakkan ya baku kunya.
Ance yin haka sai mai son KWANCIYA ko KUDI watau abin duniya.
Ance namiji YAFI mace yawan shekaru namiji da mace shi ne zaman lafiya.
Ance wadda ta dade bata yi aure ba, ko bazawara ba abin da zaa tsinta a jikinta!
Ance YARINYA ko wadda namiji ya girma ta fijin magana, don RASHIN SANIN yanayin halitta.
Ance kwarya ta bi kwarya saboda idan ba haka ba, akwai matsala, sai ka ce babu matsala idan AN BI.
Matsala RASHIN FAHIMTA ke kawowa ba shekaru ba.
ANYA AKWAI CIKKAKE ILIMI a abin da WASUN SU KAN CE?
WALLAHI BABU!
To ya za'a yi, wadanda suka fi TSORON DUNIYA fiyye da tsoron lahira su yarda suyi irin wannan auren?
Ai dole suji tsoron wulakanci, da zagi, da adawa da zargin da za'a yi masu a nan duniya!
Amma tambaya a nan shi ne, HAKA ZAMU CIGABA?
A MUNAFUNCE?
Abin da yasa nace hakkan shi ne akwai da yawa mutanen da suke so suyi irin wannan auren na tazaran shekaru, amma suna tsoron hukuncin alummah a kan su...kuma abin mamaki da tsoro INDA MUSULMI su ma ne gaba wajen yanke hukunci da kyamar wannan matsayi na auren tazara!
Tabbas duk inda alummah take akwai mutanen KIRKI akwai kuma na BANZA!
Saboda haka akwai masu auren YAUDARA akwai kuma masu SAKACIN da za'a yaudare su, saboda su ma a YAUDARE suke nasu niyyar ta auren.
Sunyi ne don kawai SAMUN YADDA suke so da wanda suka aura.
Watau NIYYAR su ba mai kyau bane.
Kamar ace idan MACE mai niyyar auren namijin da ta girma, tayi ne da niyyar ta ci mafanin yarintar shi ko don ace ta cire tuta, ta hadu wannan Allah Ba Zai bata ikon dorewa a hakkan ba...hakki zai fito.
Ko kuma mace ta so ba mijin wahala tare da rashin mashi LADABI, ko DAA kuma da kallon shi a bai isa ba, to wannan babu amfani, kuma da zaran namijinya fahimci haka zai gane kuma ya kaurace mata.
Irin wadannan matan ne suke zuga masu NIYYAR yin aure don Allah da kada su yi.
Tabbas yadda ake da miyagun maza haka ake da mata miyagu wadanda zasu rinka wa abokan aure gwale gwale da kudi watau abin hannun su don sa su abin da suka ga dama.
Wannan bai yi ba.
Amma ba shi zai sa a daina auren ba...tunda matan basu taru sun zama daya ba...duk da yawancin mata akwai mugun son kai...amma ilimi da hankuri zai iya sa wasu da yawa su fahimtu.
Haka zalika akwai maza masu auren yara saboda su farfado da zamanin yarintar su da ke nema ya bar su ta hanyar wassanni, da kuma samun nishadi, tun da haka suke.
Irin wadannan maza suma ai ba son Allah da Annabi suke wa yaran matan ba, illah son kai, amma nasu ance NORMAL ne don ba'a da gaskiya.
Allah Bai umurce mu muyi amfani da shedan wani mahaluki fiye da shaidar Shi ba...kamar na yadda Ya Hukunta auren Annabi SAW, da Khadija domin Ya San nan gaba zamu so koyi da wannan hukuncin.
Amma har yanzu muna kyaran wannan hukuncin saboda haka dole ne alummah ta cigaba da rikicewa domin za'a samu mutane da yawa suna son juna amma tazaran shekaru ba zai bari ba suyi aure ba sai dai zina a boye.
Idan dai MATA zasu ki KORAFI watau GORI, SON KAI, ROWA da ZARGIN KUDIN SU AKE SO, da gudun jikin su ake nema, ko zaa yi masu kishiya idan sun TSUFA, sun kalli cewan ba ma dole ne su kai tsufan ba.
Kuma ba su ganewa ko sun tsufa ko ba su ba Idan mijin su yayi niyya babu makawa?
Kuma wai mata masu tsoron wai kada a ya da su ace sun tsufa, watakila ba ita yake so bane, kuma ta ba da kai ba tare da adduan cewan akwai alheri ko babu ba.
Ko kawai watakila irin matan da suke gudun auren na tazara sun san su ba ABIN SO BANE maana basu da HALIN KIRKI ko kuma sun dauka TSOHO ko wanda ya girme su shi kadai ne zai masu adalci.
To wannan duk dabara ne da ya rage wa mai shiga ruwa!
Su kuma mazan da za'a iya auren, zasu kama kan su, su rage son banza, su san ciwon kan su, su kama girman su da auren, da TSORON ALLAH zasu ci ribar auren tazaran.
Kuma zasu ci nasara a rayuwa tare da gode da wannan auren kuma, akwai mutunci da daukaka a irin wannan aure domin namiji zai GIRMA tun da yarintar shi.
Ba fa tsufa ba!
Domin duk wannan labarin na TSOTSE YARINTAR mutun da wani cewan mutun yana rafkewa ya tsufa don ya auri wadda ta fi shi shekaru karya ce, ba a fada ba sunnan annabi SAW ba.
Sharri ne na makaryata da masu ZUNDE.
A karshe dai yakamata mu san HALI ne ZAMAN AURE ba Kwanciya, kudi ko shekaru ba.
Duk da wadannan suna kara danko ko nishadin auren.
Allah Sa mu dace, kuma muyi koyi da abubuwan kirki a rayuwa ba SON RAI da RAINA maganar Allah a FAKAICE ba.
0 notes
hausa24-blog · 5 years
Text
Ramadan: Marasa Galihu 271 Su Ka Ci Moriyar Asusun Zakka - Sheikh Argungu
New Post has been published on https://is.gd/r4B4xp
Ramadan: Marasa Galihu 271 Su Ka Ci Moriyar Asusun Zakka - Sheikh Argungu
Kimanin marayu da fakirai dari biyu da saba’in da daya (271) ne suka ci moriyar asusun zakka da wakafi na karamar hukumar mulki ta argungu a shekarar bana a karkashin jagorancin Alhaji Umar Gero Kangiwa (Sa’in Kabi).
Malam Muhammadu Ba’are (MUHAMMADU GURU) yana daga cikin bayin Allah da suka ci moriyar wannan shirin Kuma ya shedawa wakilinmu da cewa ya gode wa wannan kwamitin bisa ga irirn jajircwar da ya yi wajen ganin ya karbo zakka daga hannun attajirai ya baiwa mabukata, inda ya yi addu’ar Allah ya kara basu kwarin gwiwa wajen aiwatar da wannan aikin Kuma ya saka musu da alheri.
Shugaban kwamitin Zakka da wakafi na jihar Kabi, Dattijo Alhaji Muhammad Kwaido ya halarci taron wanda aka gudanar a fadar Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera CON. Kuma ya bayyanawa wakilinmu da cewa a wannan shekara sun soma ne da Karamar Hukumar Mulki ta Augie inda suka raba zakkar gero (hatsi) sai gundumar Gulma inda suka raba gero da kudi daga nan sai Dakingari the nda suka raba kudi sai Kuma nan Argungu inda suka raba atamfa, shinkafa man gyada da kudi ga marayu da fakirai.
Kwaido ya cigaba da cewa suna zagayen ne don su tabbatarda an baiwa wadanda Allah ya ba da umarnin a baiwa sannan Kuma ba a yi sonrai a cikin aikin ba.
Ya bayyana gamsuwarsa bisa ga yadda rabon kayan ke gudana sai dai ya nuna tashin hankalinsa bisa ga yadda mutane ke kyamar bayar da zakka duk da ya ke mabukata sai karuwa suke yi saboda haka ya yi kira ga masu hannu da shuni da su ji tsoron Allah su rinka bayar da zakka, duk da ya ke an sani suna da ‘yan uwa da mokota mabukata amma duk da haka yana da kyau su rinka tsakuro wani abu suna sakawa a asusun zakka da wakafi don kaucewa zargi.
Har wa yau dai Kwaido ya ambaci Alhaji Muhammadu Jiga Sarkin Noma a matsayin wanda ya fi kowa fitarda zakka a jihar Kebbi bisa ga kididdigar kwamitin Zakka da wakafi na jihar Kebbi saboda a duk lokacin da zai fitar da zakka sai ya nemi malamai tare da wannan kwamitin don su bayyana masa adadin da ya kamata ya fitar sannan kuma idan ya fitar yakan bayar da ita inda ya kamata.
Daga karshe Kwaido ya yi kira ga sauran kananan hukumomi da su yi koyi da Augie, Argungu, Suru, Dandi da wadansu sassa na kananan hukumomin Gwandu da Birnin Kebbi wajen farfado da kwamitocin zakka don karbo zakka da Kuma raba ta ga wadanda Allah ya ce a baiwa.
Da ya ke zantawa da wakilinmu, Sa’in Kabi Alhaji Umar Gero Kangiwa bayan kammala taron rabon kayan, ya ji dadin yadda masu hannu da shuni ke karba kira wajen sauke nauyin da Allah ya dora musu na taimakon marayu da fakirai sabanin shekarun baya inda a duk lokacin da suka je karbar zakka sai masu kudin suna bata rai wadansu Kuma kafin su bayar sai an kai ruwa rana yayanda wadansu ba su ma bayarwa.
Ya ce wannan kwamitin na mutum bakwai tun kafin azumin kowace shekara ya kan soma aiki ba dare ba rana don zakulo marayu, fakirai, miskinai da duk wadanda Allah ya bayar da umarnin a baiwa don sauke nauyin da shari’a ta dora musu.
Liman Isah Abubakar limamin masallacin izala na sabongarin Kanta ya bayyanawa wa wakilinmu da cewa wannan aikin taimakawa marayu, gajiyayyu, miskinai da zawarawa ana yin sa tun lokacin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam wanda tun wannan lokacin akan rubuta sunayen marayu ana yi musu ihsani daga aljihun baitulmali Kuma idan lokaci zakka ya yi akan ba su, hasali ma ranar da magidanci ya rasu Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam ya kan yi umarni da a kaitallafi a gidan musamman na abinci saboda a saukaka wa iyalinsa damuwa saboda haka yin haka koyi ne da shi saboda yana rage damuwa ga marayu musamman a lokacin bukin Sallah, an bayarda sutura, shinkafa da mai da kuma kudi wannan ba karamin alheri ba ne.
Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce “Mafi alhairin gida shi ne gidan da akwai maraye kuma ana tausaya ma sa haka Kuma mafi sharrin gida shi ne gidan da akwai maraye kuma a na munana ma sa.”
Saboda haka Malam Isah Abubakar ya yi kira ga shugabanni da su cigaba da wannan aikin na alheri kada su yi kasa a gwiwa saboda alheri yana sauka a cikin al’ummar da ake tausayawa marayu kuma Allah yana tsareta daga bala’o’i.
Wadanda dai su ka sami tallafin sun hada da marayu 140, fakirai 131, Guragu 40, Makafi 40, Kutare 15, sannan kuma da limamai da ladanai.
Hakazalika shi ma kwamitin tallafawa marayu na Kungiyar izala ta karamar hukumar mulki ta argungu a karkashin jagorancin Alhaji Suleman Muhammed (Jarman Kabi) da Alhaji Garba Tungar Marina (GGT) ya tallafawa marayu da dama kamar yadda yadda yadda saba a kowace shekara.
0 notes
isausmanmohd · 2 years
Photo
Tumblr media
Gaskiya ya dace likitoci su hada kai da Malaman Addini wajen wayar da kai akan wannan Musiba na yin "Bleaching" da ya zamo ruwan dare ayau, domin akasarin masu yin basu da masaniya akan fitinar da suke jefa kawunansu cikin abinda ya shafi makomar lafiyarsu, da kuma lahirarsu, a gefe guda kuma duk zukatan dake da burbushin imani, na matukar kyamar hakan kuma masu yin basu birgesu. ALLAH ya kawo sauki, ALHAMDULILLAH https://www.instagram.com/p/Cp13IBaos1v/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
newssplashy · 6 years
Text
Ziyarar Super eagles zuwa villa: Buhari yayi kira ga yan wasan Super eagles gabanin gasar cin kofin duniya
A jawabin sa yayin da suka ziyarci fadar shi ranar laraba 30 ga watan Mayu, shugaba Buhari yayi kira ga yan wasan da su kasance abun koyi kasancewar su na zama yan wasa mafi karancin shekaru da zasu kara a gasar kofin duniya a tarihin Nijeriya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karbi bakoncin yan wasan kwallon Nijeriya inda ya ja kunnen su gabanin karawar su a gasar cin kofin duniya.
Yan wasan Super eagles tare da wasu jami'an hukumar kwallon kafan Nijeriya ta NFF sun kai masa ziyara ne don neman yardar sa kafin su zarce gasar.
 A jawabin sa yayin da suka ziyarci fadar shi ranar laraba 30 ga watan Mayu, shugaba Buhari yayi kira ga yan wasan da su kasance abun koyi kasancewar su na zama yan wasa mafi karancin shekaru da zasu kara a gasar kofin duniya a tarihin Nijeriya.
Shugaban ya gargade su da su sani cewa zuwan su Rasha, suna masu daukaka tutar kasar tare da jagorantar dinbim jama'ar kasa.
Yayi kira da su kasance masu kwatanta adalci yayin buga wasanni ba tare da nuna wariya ko kyamar wadanda zasu fuskanta.
 A jawabin sa, mai horas da yan wasan Nijeriya, Gernot Rohr ya shaida ma shugaban cewa zasu iya bakin kokarin su wajen daga martaban Nijeriya a gasar.
Shima jagoran yan wasan, Mikel Obi ya jaddada magana sa inda ya kara da cewa zasu yi kokarin cin kofin.
Mikel ya kuma bayyana cewa zasu jajirce a gasar kasancewa a wannan karo hukumar kwallo ta biya su dukanin alwus da ya kamace su kafin su zarce zuwa gasar. Yace wannan matakin zai kara baiwa yan wasan karfin gwiwa wajen buga wasa tare da kare martaban Nijeriya.
Bayan ziyaran da su kai fadar shugaban, yan wasan sun zarce zuwa birnin London inda zasu kara da kasar Ingila da Czech Republic a wasanin sada zumunci gabanin gasar kofin duniya wanda zata fara ranar 14 ga watan Yuni.
Nijeriya tana rukuni daya da kasar Argentina da Iceland da kuma Croatia.
Yan Nijeriya sun mika tutar kasar ga tawagar domin su daga ta ga idon duniya a gasar.
source http://www.newssplashy.com/2018/05/ziyarar-super-eagles-zuwa-villa-buhari.html
0 notes
isausmanmohd · 2 years
Photo
Tumblr media
ABINDA YASA AKE TSANGWAMAR ALMAJIRAI. Akan kawar da kai, tare da runtse idanu daga barin duba izuwa ga dimbin matsaloli da kura-kurai dake kewaye da yadda ake karatun Boko, saboda kasancewarta karatune na sana'a, kuma ananne ake bayar da shaida da ake samun aiki a hukumance, kuma Gobnati na sanya hannu cikin bayar da kulawa, mutanenmu na yau kuma 90% yan jari hujjane, tunaninsu yafi karkata ga abinda suke ganin ribarsa a zahiri, ta hanyar rashin damuwa da wanda ribarsa ke a lahira. Ana kokarin zuzutawa, tare da karin gishiri ga matsalolin da ke kewaye da harkar Almajiranci tare da kokarin kitsa makirce-makirce domin ganin sai an dakushe wannan harka domin anan ba'a bayar da wata takarda ta shaida wacce dalilinta za'a iya samun wani aiki a hukumance. Dalilin hakan sai su kuma makiya karatun Kur'ani (Daga Yammaci) sai su shigo ta bayan danga, suke kitsa hudubobi domin cusa kyamar wannan harka a zukatan mutane (Ta hanyar bayar da kwangiloli) wannan shine sila ko dalilin kyamar Almajiranci. Muhammad Usman Gashua✍️🙏 ALLAH YA SHIRYI MASU WANNAN MUGUWAR AKIDA, YA SHIRYESU ALFARMAR MANZON ALLAH (S.A.W). ALHAMIDULILLAH. https://www.instagram.com/p/CpxrNHEoBCr/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
isausmanmohd · 2 years
Photo
Tumblr media
MUNA ALLAH WADAI DA MANAKISAR DA AKE MA ALMAJIRAI A WANNAN SHIRI NA "MANYAN MATA" Bama musawa, lallai duba ga yanayin chanjawar zamani da bukatar samun gyare-gyare a harkar Almajiranci, amma irin wannan salo da tashar @arewa24channel ke bi na kokarin cusa kyamar harkar Almajiranci a tunanin al'umma ta hanyar amfani da irin wadannan fina-finai da ake nuna Almajirai ne ke rikidewa su dawo bata gari dake addabar Al'umma, lallai wannan wani yakine shiryayye da aka tunkari Almajirai da shi, kuma babban manufar shine yaki da karatun Alkur'ani. A mai-makon su shagala da shirya Fim wanda ciki za su ke jan hankalin Shugabanni akan su kula da harkar Almajiranci ta hanyar sanya hannu wajen tallafawa sha'anin, amma sai al'amarin na su ya zamo Almajirancin suke son yaka kai tsaye su kawar da shi. Muna masu kiransu da yaren da zasu fahincemu, lallai da bukatar su dakatar da wannan mummunan kudurinsu na su na kwangilar Yahudawa, domin lallaine ba'a kawo gyara ta hanyar muzantawa da kuma cin fuskar wadanda ake so a gyarawa. MUNA FATAN SAKONMU ZAIJE GARESU, KUMA ZASU DAUKI MATAKIN KAWO GYARA. Muhammad Usman Gashua✍️🙏💔 ALHAMIDULILLAH. https://www.instagram.com/p/CpoCRWgIk95/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
isausmanmohd · 2 years
Photo
Tumblr media
Sufaye basu noma gonar gaba, balle su girbi tsiron kiyayya, basu cinikayyar kyamar juna, balle su ribatu daga husuma, bal dai suna noma gonar hakuri ne, domin su girbi nasara, sannan suna cinikayyar kyautata zato ne domin cin ribar kyautata alaka da halitta. Su na musanya sharri da alkairi ne domin neman yardar ubangijin halitta, suna ado da kawaici domin samun kamalar zati. Kada mu bari siyasa da 'yan siyasa su kutsa tsakanin katangar 'yan uwantaka dake tsakaninmu su rusheta, Hailala, Salati da Istigfarin da muke su zamo ma'aunai da zasu bambantamu da wasunmu a dabi'a, rigar ashariya da zagi sam batayi dai-dai da siffa ta rigar Sufaye ba, kuma ba tarbiyar gidan Sufanci bane hakan. AYI HAKURI DAN ALLAH AYI MU'AMALA TA MUSULUNCI CIKIN YANAYI NA AMINCI DA KUMA SABANI. ALLAH YA BARMU DA SON MANZON ALLAH (S.A.W). ALHAMDULILLAH https://www.instagram.com/p/Co4uIrJIFCp/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
isausmanmohd · 2 years
Photo
Tumblr media
KA GIRMAMA KOWA, AMMA KA RIBANYA GIRMAMAWARKA GA "MAHAIFIYA" Babin rayuwar kowa yayin gagwarmayar kaiwa zuwa ga nasara cike yake da kadaici, tsangwama, hantara,kyama da kuma kalubale daga dukkanin kusurwowi, amma babin farko na samun nasarar kowa, mutane zasu dinga ketowa. Martabawa, girmamawa da soyayya shine abinda zai ke bayyana a tattare da su gareka. Ashe dai a hakika mutane ba suna ki ko kyamatar zatin mutane ba ne, ba kuma suna girmamawa ko kaunar zatin mutane ba ne, suna ki da kyamar duhun dake tattare da su ne, sannan kuma suna zumudin son amfana da hasken dake tattare da su ne.( Wato soyayyarsu gareka dalilinta haskenka, kyamarsu gareka dalilinsa duhunka). Amma ita Mahaifiya itace take cike gibin dake a tsakani na sanin kimar zatinka, soyayyarta gareka sam ya girmi ajin dalili, tun daga busa numfashin ka na farko, burinta ta haskaka rayuwarka da hasken kauna dake fitowa cikin zuciyarta, bata san duhunka ba, balle sadda ka riski haske wani abinka ya rudeta, kuma ba ta da ranar da zata daina kaunarka, ko kuma ta gujeka saboda wani abinda kake tattare da shi ya kubce maka. Mai yiwuwa shi yasa ko a hadisi yazo, ko da mai tambaya ya tambayi ANNABI (S.A.W) Shin wa zai yiwa biyayya akan kowa, Sai yace da shi "Mahaifiya" yana fadi yana nanatawa kafin ya ambaci waninta. (Muhammad Usman Gashua✍️) YA ALLAH KA TSAREMU SABAWA IYAYE, KA BAMU IKON SANYAYA DUBANSU GAREMU. ALHAMDULILLAH. (at Nigeria) https://www.instagram.com/p/CoehmAPIffs/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
isausmanmohd · 2 years
Photo
Tumblr media
HAKAN NA DAGA "MISALAI" DAKE NUNA CEWA .........! Shekaru sama da 45 aka shafe, Gobnatin Ahli-Saud ta dauki nauyin samar da Kungiyoyi a kasashen Duniya, wadanda suka bazama lungu da sako domin ganin sun yaka, tare da kawar da "DARIKUN SUFAYE". Misali, Kungiyar Izala a Nigeria, ta shafe sama da shekaru 45, cikin zimmar yakar Darikun Sufaye, musamman Darikar Tijjaniyya a yankin yammacin Africa, tare da ganin ta mayar da ita tarihi. Gobnatin Ahli Sa'ud, tayi amfani da wasu hanyoyi domin ganin ta dakile Darikun Sufaye kamar:- • Bayar da guraben karatu kyauta ga matasa zuwa jami'oinsu domin juyar musu da Akida zuwa Wahabiyanci. • Wallafa litattafai ana rabawa kyauta, wadanda suke kunshe da zallar karantarwa na akidojin Wahabiyanci da cusa kyamar Sufanci. • Bude tashoshin gidajen Rediyo da na Telebijin domin ganin an cusawa al'umma kyamar Sufanci da Sufaye ta hanyar karantar da Wahabiyanci. • Bayar da tallafin kudi ga jagororin Kungiyoyin da suka samar, tare da agaza musu cikin tafiyar da dawainiyarsu. • Da sauransu. Anyi amfani da salon kage, sharri, kazafi, da kuma yarfe gami da Makirci, Munafurci da zalinci duk domin ganin an dakile Sufaye ta fuskoki mabambanta , amma sai gashi anje an dawo, ayau ALLAH ya kawo chanjin al'amari, ita dai wannan Gobnatin itace ke neman hada hannu da Sufaye (Tijjanawa) tana mai nuna nadamarta ta hanyar bayyana irin falalar da ALLAH yayiwa Tijjanawa tare da bayyana Adadinsu da yake nusar da cewa "SAM YAKARSU DA AKAYI TSAWON ZAMANI BAIYI TASIRI BA". Ko da yake dama hakan ba abin mamaki bane domin MANZON ALLAH (S.A.W) yace " لا تزال طائفة من أمتي على الدين ظاهرين لعدوهم قاهرين، لا يضرهم من خالفهم إلا ما أصابهم من لأواء حتى يأتيهم أمر الله. ( Muhammad Usman Gashua✍️) ALLAH YA TABBATAR DAMU AKAN WANNAN TAFARKI, YA KARBEMU MUNA TIJJANAWAN KWARAI. ALHAMDULILLAH. https://www.instagram.com/p/Ch71S5yIbOl/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
bbchausa · 5 years
Video
undefined
tumblr
Najeriya da Afrika ta Kudu sun tattauna kan kyamar baki https://www.youtube.com/watch?v=dzH-sthqF1U
0 notes
voahausa · 4 years
Link
A yau Talata dangi da abokai su ke yiwa George Floyd bankwana na karshe a tsare-tsaren jana’izarsa da za a yi a birnin Houston,  makwanni biyu bayan mutuwarsa a hannun ‘yan sanda, abin da ya sake ta da zanga-zanga a birane da dama na Amurka na nuna kyamar wuce gona da iri da ‘yan sanda suke yi. Bayan addu’oin, ‘yan sandan birnin Houston za su yi jerin gwano su raka tawagar zuwa birnin Pearland inda za'a binne Floyd a kusa da kabarin mahaifiyarsa. An kunna wutar zauren majalisar birnin a daren jiya Litinin da launin ruwan kwai da zinari, kalar makarantar da Floyd ya yi, domin tunawa da rayuwarsa. Sauran birane sun bi sahu da kunna wuta da wadannan launuka da suka hada da biranen Los Angeles, Boston, Oakland, Las Vegas, New York da sauransu. An ba sauran jama’a damar karrama Flyod ta karshe jiya Litinin inda dubban mutane suka yi tururuwa a majami’ar Praise, wurinda aka bude akwatin gawarshi. An kuma yi addu’oin tunawa da shi a biranen Minneapolis da kuma Raeford.   via Voice of America Hausa
0 notes